A jawabin da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Emmanuel Udom ya yi was mutanen jihar, ya ce gwamnati ba zata rufe makarantun jihar ba tunda babu rahoton cutar a jihar.
” Bari in sanar muku yau cewa babu rahoton cutar coronavirus a wannan jiha. Saboda haka ba zamu rufe makarantun mu ba, amma za mu maida hankali waje ganin cutar bata shigo mana ba.
Jihar Akwa-Ibom ta kakkafa wurare domin ko da za a samu wani da ya kamu da cutar a jihar. Mun samar da motocin daukan marasa lafiya a ko-ina a fadin jihar domin shirin ko ta kwana.
Udom ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da wayar da kan mutanen jihar hanyoyin kiyaye kai yadda za kiyaye daga kamuwa daga cutar.
Idan ba a manta ba sakataren ma’aikatar Ilimi, Sunny Echono ya bayyana cewa gwamnati ta umarci duka makarantu a kasar nan, Kama daga Jami’o’i ne, Kwalejojin Ilimi, makarantun Sakandare, Makarantun Firamare duk su rufe makarantun har sai lokacin da gwamnati ta ce a dawo.
Dama Kuma Idan ba a manta ba gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma sun sanar da rufe duka makarantun yankin saboda cutar coronavirus din a ranar Laraba.
Jihar Legas da wasu Jihohin Kasar nan duk sun bi sawu suma.
Sakatare Echono ya ce zuwa ranar Juma’a za a fadi ranar da za a bude makarantun.
A ranar Alhamis shugaban Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ya gargadi kasashen Afrika da su maida hankali matuka kan wannan cuta, da kirkiro hanyoyin dakile yaduwar cutar.
Ya ce idan ba amaida hankali ba cutar za ta yi muni a Nahiyar.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da su karfafa matakan hana yaduwar cutar duk da cewa masana kimiya na gab da gano maganin cutar.
Ghebreyesus kungiyar za ta ci gaba da tallafa wa kasashen da basu da karfin samun kayan gwajin cutar.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne WHO ta sanar cewa mutane 400 sun kamu da cutar a kasashen Afrika inda 41 daga cikin su sun warke.
Sannan a Najeriya mutane 8 ne ke dauke da cutar zuwa yanzu haka.
Kwayoyin cutar CoronaVirus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.