An tabbatar da cewa mutum na 51 da ya kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, ya kamu ne a Jihar Ribas, kamar yadda Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa ta bayyana.
Hakan ya zo daidai lokacin da Gwamna Nysom Wike ya bada sanarwar hana dukkan motoci da babura shiga cikin Jihar Rivers ko kuma fita daga jihar.
Sannan kuma an hana jiragen ruwa ko kwale-kwale shiga ko fita jihar, haka ma an hana sauka da tashin jiragen sama har sai yadda hali ya yi.
Mutum 51 Ya Kamu A Najeriya: Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta bayyana cewa a yanzu mutum 51 suka kamu da cutar a Najeriya.
Sanarwar ta zo daidai lokacin da ake ta bai wa Najeriya shawara a tsaida komai da komai, kowa ya zauna a gida.
Tuni dai jiragen sama sun daina shiga da fita a Najeriya, kamar yadda sauran kamfaninin jiragen sufuri irin su Peace Air da Dana duk suka daina sauka da tashi.
NCDC ta ce zuwa yanzu wadanda suka kamu a jihar Lagos sun kai 32, Abuja 10 sai kuma jihohin Bauchi, Oyo, Ekiti, Edo, Osun da Rivers kowace mutum daya.