Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta hanzarta bai wa kowane magidanci naira 10,000 kyauta domin rage kuncin halin zaman gida da za a shiga ko aka fara shiga sanadiyyar Coronavirus.
Atiku, wanda shi ma dan sa daya ya kamu da cutar, ya bada wannan shawara ce a ranar Laraba, ganin yadda gwamnati ta dauki aniyar killace kowa da kowa a kasar a gida.
Kiran na Atiku ya zo daidai lokacin da kasar Amurka za ta ware naira tiriliyan 1 domin samar da tallafi ga al’ummar kasar a wannan mawuyacin halin da ake ciki.
Sannan ita ma kasar Canada ta ware dala milyan 82 domin taimaka wa masu kananan kasuwsnci da ruguguwar Coronavirus ya durkusar.
Atiku ya ce akwai akwalla magidanta milyan 30, ko gidaje milyan 30. Don haka idan aka fito da tsarin ba su wannan tallafi, zai taimaka kwarai a wannan yanayi da kowa ya tsinci kan sa.
Sauran Shawarwarin Atiku 5
Duk kamfanonin wayar selula su na masu lambobin waya kyautar katin waya a ba naira 1,500. Wannan zai yi amfani a lokacin takaita zirga-zirga da gwamnati ta bada sanarwa.
Gwamnati ta hada kai da kamfanomin waya domin a samar da tsarin yadda za a tura wa magidanta wannan naira 10,000 ta asusun kowane bankunan masu ajiya a saukake.
Duk wasu manyan masana’antu da cibiyoyi da kuma gidauniya-gidauniya, har da sauran manyan masu hali, su gaggauta bayar da agaji domin a tallafa wa al’umma a wannan mawuyacin hali.
Atiku ya bada gudummawar naira milyan 50 ta hannun Gidauniyar Priam GNP.
Shawara Ta 6
Atiku ya ce kada Majalisar Dattawa da ta Tarayya su je su boye kawai a gida. Su kwana da shirin cewa duk lokacin bukatar yin wata dokar gaggawa wadda za ta taimaka wajen dakile Coronavirus ta taso, to sai su garzaya su je Majalisa, su amince da kudirin, domin ya zama doka.