Najeriya ta tabbatar da karin mutum biyar masu dauke da cutar Coronavirus.
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa ce ta bayyana haka a yau Litinin, a shafin ta na Twitter cewa an samu karin mutanen biyar ne a Abuja mutum biyu, Lagos mutum biyu sai kuma da kuma Jihar Edo inda aka samu mutum daya.
An tabbatar da cewa karin mutane biyu da aka samu daga Abuja, su na daga cikin matafiyan da suka dawo daga Ingila kwanan nan, lokacin da cutar ta yi kamari a can.
Ana jin cewa dan Atiku Abubakar da ya kamu daga cutar, na daya daga cikin wadanda ake cewa sun kamu a Abuja din.
Kin Killace Kai
Babban Darakatan Cibiyar Kula da Cututtuka, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana laifin karuwar yaduwar cutar daga matafiyan da suka dawo ne daga kasashen da cutar ta Coronavirus ta yi muni sosai, saboda sun ki killace kan su, kamar yadda aka yi musu gargadi.
A wata hira da aka yi da shi a Litinin din nan da safe, a gidan talbijin na Channels, Ihekweazu ya ce babbar matsalar Najeriya ita ta ce masu dawowa daga kasashen waje.
Daga nan sai ya shawarci dukkan masu aiki a kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kan su su zauna su na aiki daga gidajen su.
Sannan kuma ya ce kowa ya yi kaffa-kafda da taka-tsantsan, domin nan gaba za a kara samun rahotannin wadanda suka kamu da cutar.
Ya nuna yi bayani a kan kokarin da ake yi din zakulo sauran wadanda suka Shiva jirahe daya da wasu da suka kamu.