CORONAVIRUS: An samu karin mutum 4 da suka kamu a Najeriya, Yanzu 139

0

Hukumar NCDC ta sanar cewa wasu mutum hudu sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya a yammacin ranar Talata.

Idan ba a manta ba hukumar ta bayyana cewa wasu 4 sun kamu da cutar a sakamakon da ta bayyana da safiyar Talata.

3 a Abuja, 1 a Legas.

A yanzu dai mutum 139 ne ke dauke da cutar, 9 sun warke, biyu sun mutu.

Lagos- 82
FCT- 28
Oyo- 8
Osun- 5
Ogun- 4
Kaduna- 3
Enugu- 2
Edo- 2
Bauchi- 2
Ekoti- 1
Rivers-1
Benue- 1

Shugaban Hukumar NCDC ya bayyana cewa an kafa sabbin wauraren gwajin cutar a wurare da dama a kasar nan. Saboda haka za arika samun mutane da dama da za ayi wa gwaji yanzu.

Sannan kuma yanzu ana bi gida gida ne domin duba yan uwan wadanda suka kamu ko kuma suka yi cudanya da wadanda suka kamu.

Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.

A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya ranar lahadi ya ce gwamnati ta saka dokar garkame garin Abuja da Legas na makonni biyu har sai an kammala yin gwajin wadanda ake zargin sun kamu da cutar.

Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.

Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukumar

Share.

game da Author