Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa an samu karin mutane hudu da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Kwamishinan kiwon lafiya, Akin Abayomi ya sanar da haka a hedikwatar ma’aikatar ranar Alhamis yana mai cewa mutane 12 kenan ke dauke da cutar a Najeriya.
Mutum daya daga cikinsu ya warke.
Abayomi yace ma’aikatan kiwon lafiya sun gano cutar a jikin wadannan mutane a dalilin yi wa mutane gwajin cutar domin gano wadanda suka kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da masu dauke da ita.
“Mun yi wa mutane 19 gwajin cutar tare da wasu mutane biyar da suka yi mu’amula da wadanda suka kamu da cutar inda sakamakon gwajin ya nuna cewa hudu sun kamu da cutar.
“’Yar Najeriya da ta dawo daga kasar Faransa a jirin saman Turkishi Airline ranar 14 ga watan Maris, wani namiji mai shekaru 50 da bai taba tafiya zuwa kasar waje ba, wani dan Najeriya da ya dawo daga kasar Jamus ranar 13 ga watan Maris a jirgin saman Luftansa na cikin mutanen da aka gano suna dauke da cutar.
Abayomi yace an kwantar da wadannan mutane a asibiti sannan har an fara yi wa mutane 1,300 gwajin cutar domin ganin ko akwai wadanda suka kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da su.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa mutane takwas sun kamu da cutar coronavirus.
Bincike ya nuna cewa mafi yawan wadannan mutane na da tarihin tafiya zuwa kasashen Amurka da UK.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.