Ma’aikatar yin bincike kan cututtuka ta sanar cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Ma’aikatar ta ce mutum uku daga cikin suna Abuja sannan 7 a jihar Legas. Ma’aikatar ta ce dukan su sun shigo da cutar daga kasashen waje ne a ‘yan kwanakinnan banda guda daya da ya kamu ta hanyar mu’amula da mutane ne.
Yanzu an samu karin yawan wadanda suka kamu a Najeriya zuwa mutane 22 kenan.
Dukkan su na killace a na duba su.
Akalla mutane 12 ne suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya in da wasu 1300, suna killace ana yi musu gwaji. A jihar Katsina ma ana yin gwajin jini wani da ya dawo daga kasar Malaysia da ake zaton yana dauke da cutar.
A dalilin Haka muka kawo muku hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.
Discussion about this post