CORONAVIRUS: An sallami marasa lafiya biyar a Legas

0

Gwamnatin jihar Legas ta sallami wasu marasa lafiya biyar da suka warke da daga cutar coronavirus.

Yan zu an samu akalla mutane 8 kenan da suka warke daga cutar.

Wata da aka sallama ta bayyana cewa bata dauka za ata rayuba tunda aka tabbatar mata cewa ta kamu da cutar.

Oluwaseun Osowobi, ta ce ta kamu da cutar ne a kasar Birtaniya bayan ta halarci wani taron Commonwealth a Landan.

Ta ce ta wahala matuka, domin ta yi fama da amai, zaswo, ciwon kai, zazzabi, da sauransu.

” Akullum sai an dirka min magani, 10 da safe 12 da rana sannan akalla 10 da da dare.

” Ma’aikatan asibiti sukan duba ni akai akai. Na ga tashin hankali matuka. sannan ina rokon ‘yan Najeriya su garzaya su je a duba su sannan a basu magani.

” Ina cikin farinciki kuma ina murnanr gaya wa duniya cewa Allah ya bani lafiya. Sau biyu ake duba ni bani da coronavirus bayan wahalar cutar da na yi fama da ita . Yanzu an sallami zuwa gida.

Zuwa ranar litini mutane 111 ne suka kamu sa wannan cuta a Najeriya. Mutum biyu sun rasu sannan an sallami mutane biyar.

Share.

game da Author