CORONAVIRUS: An rufe makarantun a jihar Bauchi kaf

0

A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe makarantun Boko da na Islamiyya na gwamnati da masu zaman kansu a jihar domin hana yaduwar zazzabin lassa da coronavirus a jihar.

Gwamnan jihar Mohammed Bala ya sanar da haka a taron tattauna hanyoyin dakile yaduwar zazzabin lasa da coronavirus tare da sauran cututtuka a jihar da ya yi da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnati.

Bala yace hana taron mutane sama da 50 a wuraren bauta a jihar na daga cikin shawarwarin da gwamnati ta yanke.

Gwamnan ya yi kira ga mutanen jihar da su dukufa wajen yin adu’o’I tare da rokon Allah gafara domin Allah ya kawar da wannan cuta a duniya.

Bala yace gwamnati ta kafa kwafa kwamiti wanda mataimakin gwamna Baba Tela zai shugabanta sannan kwamitin za ta kirkiro hanyoyin wayar da kan mutane da dakile yaduwar cututtukan coronavirus da zazzabin lassa a jihar.

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta jihar Bauchi ta bayyana cewa ta dibi jinin mutane 241 inda sakamakon gwajin ya nuna cewa 39 na dauke da cutar sannan mutum daya ya mutu.

Bayan haka wasu Iyaye da suka kai ‘yayan su makaranta ko kuma suka aika da ‘ya’yan su makaranta ranar Litini da safe sun ce sun yi mamaki yadda gwamnati ta rufe makarantu ba tare da ta sanar wa mutane ba a jihar.

Sai dai kuma a ranar Lahadi ne gwamnati ta bada wannan sanarwa cewa daga ranar Litinin duk makarantu a jihar za su tafi hutu.

Wata mata da ta kai ‘ya’yanta makaranta mai suna Nafisat Aliyu, ta jinjina matakin rufe makarantu domin kare yara daga kamuwa da cutar da gwamnati ta dauka.

A Najeriya akwai mutane 32 kenan da ke dauke da cutan, biyu sun warke, sai kuma wanda ya rasu.

Idan ba a manta ba Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa ce ta bayyana haka a yau Litinin, a shafin ta na Twitter cewa an samu karin mutanen biyar ne a Abuja mutum biyu, Lagos mutum biyu sai kuma da kuma Jihar Edo inda aka samu mutum daya.

An tabbatar da cewa karin mutane biyu da aka samu daga Abuja, su na daga cikin matafiyan da suka dawo daga Ingila kwanan nan, lokacin da cutar ta yi kamari a can.

Ana jin cewa dan Atiku Abubakar da ya kamu daga cutar, na daya daga cikin wadanda ake cewa sun kamu a Abuja din.

Bayan haka hukumar UNICEF ta fitar da wasu matakai da kuma hanyoyin da ake bi wajen tsaftace hannaye, domin gudun kamuwa da cutar Coronavirus.

Cikin wata muhimmiyar sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi, ta kuma bayyana dalilan da ya sa ake kara matsin-lamba wajen wanke hannaye a lokutan annoba irin Coronavirus.

Share.

game da Author