CORONAVIRUS: An rufe makarantu, dakatar da sallar jam’i da taron coci a kasar Ghana

0

A dalilin karin yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a kasar gwamnati Ghana ta sanar da dokar rufe makarantu da Hana tarukka a kasar da ya hada da sallolin jam’i da taron coci.

Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya sanar da haka ranar Litini yana mai cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar zuwa makonni hudu masu zuwa.

“Daga yanzu gwamnati ta hana duk taron mutane a kasar nan domin hana yaduwar coronavirus.

“Tarukkan da aka hana sun hada da masallatai da coci, wasanni, wuraren jana’iza, siyasa da sauran su.

Bisa ga wannan doka gwamnati ta rufe duk makarantun Firamare, sakandare da jami’o’I na gwamnati da na kudi a kasar.

Za a kyale daliban sakandare rubuta jarabawar su na kammala karantun sakandare wato WAEC da na kammala aji uku da za a yi a bana.

Bayanai sun nuna cewa kafin gwamnati ta bada wannan sanarwa wasu makarantu dake kasar sun fara rufe makarantu su tun da wuri.

YADUWAR CORONAVIRUS

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne gwamnatin kasar Ghana ta sanar cewa wasu mutane biyu dauke da kwayoyin cutar daga kasashen Norway da Turkey sun shogo Ghana.

Gwamnati ta ce an killace wadannan mutane domin hana yaduwar cutar.

Sai dai kuma a ranar Lahadi shugaban fannin kiwon lafiya na kasar Badu Sarkodie ya sanar cewa an gano cutar a jikin wasu mutane hudu ‘Yan kasan.

Sarkodie yace a cikin wadannan mutane hudu akwai wata dalibar jami’ar kasar Ghana da ta dawo daga kasar Amurka.

A lissafe dai adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar sun kai shida a Ghana.

KAFA DOKAR HANA SHIGE DA FICE

Domin hana yaduwar cutar gwamnatin kasar Ghana ta kafa dokar hana shige da fice daga kasar.

“Gwamnati za ta tilasta wa mutanen da suka shigo kasar killace kansu na tsawon kwanaki 14 domin hana yaduwar cutar.

Ya kuma ce gwamnati ta hada hannu da ma’aikatan jiragen sama saboda kada ma su yi jigilan mutane daga wannan kasashe.

Share.

game da Author