Sakamakon firgita, tsoro da tararrabin yiwuwar bullar cutar, Gwamnatin Jihar Filato ta dauki matakin gaggawar kullace wasu ‘yan kasar Chana su 3 da kuma wasu ‘yan Najeriya su 39.
An killace su ne a kauyen Bakin Kaya, cikin Karamar Hukumar Wase, duk kuwa da cewa daga cikin su babu wanda aka samu ya kamu ko aka ga alamar cutar a jikin sa.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato Nimkong Ndam, ya shaida wa manema labarai a Jos babban birnin Jihar Filato cewa, an killace su ne ba don komai ba, sai saboda daukar matakin cewa wadancan ‘yan Chana ba su dade da dawowa daga kasar su can Chana.
Ya ce mutane 39 kuma duk ma’aikatan hakar ma’adinai ne a kar kashu. Ya ce dukkan su zargi ne kawai ake yi musu.
“Za a ci gaba da bibiyar su da sa-ido a kan su. Da zarar sun cika kwanaki 14 babu wanda aka samu da xuar, to za sallami kowa.
Har yau dai mutum daya aka samu dauke da cutar a Najeriya.
Kwamishinan na Harkkokin Lafiya na Filato ya ce hankula sun kara tashi ne a jihar saboda samun tabbacin cewa a ranar Laraba da ta gabata ne dan Chana din ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, daga can ya karasa Filato.