Coronavirus: An killace wasu ‘Yan kasar Chana hudu a asibitin Abuja

0

An killace wasu ‘yan kasar Chana a asibitin Abuja domin a duba su da kyau kada garin neman kiba a samo rama.

Wadannan ‘yan kasar Chana sun iso tashar jiragen saman Nnamdi Azikiwe a Abuja ranar Talata inda bayan an yi musu gwajin cutar a tashar ne aka kai su asibiti.

A asibiti sakamakon gwajin coronavirus da aka yi musu ya nuna cewa basa dauke da cutar amma an gano alamun mura kokuma cutar Nimoniya a jikinsu.

Wani ma’aikacin asibitin mai suna Sulai yace a dalilin haka aka killace su a wani bangaren asibitin na tsawon kwanaki 14 domin samun tabbacin cewa wadannan mutane basa dauke da coronavirus a jikinsu.

Sulai yace asibitin tare da hadin gwiwar kungiyar kiwon lafiya ta duniya za su bada bayanan halin da wadannan mutane ke ciki a taron tattauna cutar da za a yi ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Fabrairu wani dan kasar Italy ya shigo Najeriya dauke cutar coronavirus.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa, wannan mutum dai ya shigo Najeriya ne daga kasar Italy inda bayan kwana daya da shigowa kasan ya fara rashin lafiya.

Daga nan sai aka kai shi asibiti inda aka gano cewa ya na dauke da cutar.

Har yanzu dai babu rahotannin ko wani ya kamu da cutar a Najeriya amma cutar ta yadu zuwa kasashe 73 inda mutane 90, 000 na dauke da cutar sannan 3,000 sun mutu.

Share.

game da Author