Mahukuntan Kula da Lafiya na Jamus sun killace Shugabar Kasar, Angela Mikel a jiya Lahadi, bayan an tabbatar da wani likita da ya duba ta a cikin makon jiya din ya kamu da cutar Coronavirus.
Kakakin Yada Labaran Gwamnatin Jamus, Steffen Seibert ne ya bayyana wa manema labarai wannan hali a ranar Lahadi, jima kadan bayan da shugabar ta kammala sanarwar kakaba dokar hana taruwar mutum sama da biyu a wurin daya a Jamus.
Ya ce za a rika yi mata gwaji a kai a kai domin tabbatar da shin ta na dauke da cutar ita ma din ko kuwa.
Dokar Coronavirus A Jamus
A ranar Lahadi ne dai Shugaba Angela Mikel ta yi sanarwar hana taron da suka ya wuce mutum biyu.
An ce ba a yarda a ga mutum sama da biyu a wuri daya ba. Amma dai an amince a fita gida domin dubo maras lafiya.
Sannan kuma dokar ta hana tsayawa kusa da kusa da juna. An ce a bayar da tazarar akalla mita 1 da rabi tsakanin mutum da mutum.
Ya zuwa ranar Lahadi dai sama da murum 24,000 ne suka kamu da Coronavirus a Italy. 92 sun mutu, yayin da Kuma 266 suka murmure daga cutar.
A Jamus an hana kasuwanni da sauran wuraren cin abinci, sai dai mutum ya aika a kawo masa har gida.
Cibiyar Bincike da Tattara Alkaluma ta cikin shahararriyar Jami’ar nan ta John Hopkins University ce ta sanar da alkaluman adadin mutum 24,000 da suka kamu da Coronavirus a Jamus.