Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Osun Rafiu Isamotu ta ce an killace wasu Alkalai su 20 da suka dawo daga Dubai domin kada ko suna dauke da cutar coronavirus.
Isamotu ta fadi da haka ne ranar Laraba a wani takarda da aka raba wa manema labarai.
Ta ce wadannan alkalai sun yi tafiya zuwa kasar Dubai domin halartar taro daga 9 zuwa 13 ga watan Maris.
“Bayan sun dawo ne suka killace kan su a gidajen su domin samun tabbacin ko suna dauke da cutar.
Isamotu ta kuma ce gwamnati na sa ido domin ganin koda wani daga cikinsu ya fara nuna alamun cutar a jikin sa.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya killace kan sa tare da mika jinin sa domin a yi gwaji, bayan yayi cudanya da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugagab Kasa Abba Kyari wadanda dukkan su sun kamu da cutar.
Babban Daraktan Kungiyar Gwamnonin Najeriya Asisha Okauru ya bada sanarwar killace kan sa da iyalan sa, bayan haduwar da ya yi da Gwamna Bala a wurin taron gwamnoni.
Shi ma Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana killace kan sa tun daga ranar Talata da dare.
Hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.