Tun bayan killace dan kasar Italiya da ya shigo wa Najeriya da cutar Coronavirus ba samu rahoton wani ya kamu da cutar sai a jiya.
Hukumar NCDC ta bayyana cewa an gano wani dan Najeriya da ba bako ba ya kamu da cutar coronavirus din.
Yanzu dai yana killace a wani asibiti ana duba shi a jihar Ondo.
Shi dai wannan mara lafiyan yana daga cikin wadanda suka yi mu’a’mula da baItaliyan da ya shigo wa Najeriya da wannan cuta.
Bayan haka kuma an samu mutum na farko da ya fara mutuwa a nahiyar Afrika a kasar Masar wato Egypt.
Wanda ya rasu din dan asalin kasar Jamus ne da aka killace a wani asibiti dake kasar mai shekaru 60.
Ministan Lafiyan kasar Masar ya bayyana cewa wannan mutum ya shigo kasar Masar ne a jirgin ruwa na yawon bude ido.
Kafin wannan jirgin yawon bude Ido ya iso kasar Masar, mutane uku ne kacal aka tabbatar sun kamu da cutar. Zuwan wannan jirgin yasa an samu karin wasu da dama, da ya kai mutane 55 a kasar. 19 daga cikin su baki ne.
Zuwa yanzu akwai akalla mutane 81 da suka kamu da cutar a Afrika, Egypt 55, Aljeriya 17, Najeriya 2, Kamaru, 1 Senegal 4 sannan da kasar Tunisia 1.