Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Legas Akin Abayomi ya bayyana cewa likitoci zasu yi wa fasinjojin da suka yi tafiya a jirgin ‘British Airways BA 75’ da matar da aka gano cutar Coronavirus a jikin ta.
Abayomi ya fadi haka ne ranar Talata yana mai cewa tun bayan samun tabbacin cutar a jikin wannan mata da ta shigo Najeriya daga kasar UK likitoci suka fara gudanar da bincike domin gano wadanda ka iya kamuwa da cutar a dalilin yin mu’amula da matan.
Ya ce an hada da ‘yan uwan wannan mata an killace su na tsawon kwanaki 14.
Abayomi ya musanta korafin da wasu ke yi cewa sai da aka bari cutar ta kama matar sannan aka yi mata gwajin cutar.
Ya ce duk wannan ba haka bane domin daga isowarta Najeriya aka yi mata gwajin cutar inda dole sai da aka jira sakamakon.
Sannan ma’aikatan hukumar NCDC da kar suka gano gidan matar bayan sakamakon gwajin ya fito.
Bayanai sun nuna cewa an bar matar da ‘yan uwantan zaune a motar daukan marasa lafiya a dalilin rashin ma’aikacin da zai duba su.
KARUWAR MUTANEN DAKE DAUKE DA CUTAR:
Abayomi ya ce akwai yiwuwar samun karuwar mutanen da ke dauke da cutar a kasar nan.
Ya fadi haka ne ganin yadda aka killace mutane uku baki wanda ake zargin suna dauke a cutar a asibitin kula da masu fama da cutar a jihar.
Abayomi yace mutum na farko ya shigo Najeriya ranar Litini ne daga kasar Amurka inda daga zuwansa aka gano wasu alamun cutar.
“An debi jininsa sannan muna jiran sakamakon gwajin a yanzu haka.
Na biyu ya shigo Najeriya ranar Talata daga kasar UK inda shima na dauke da wasu alamun cutar a jikin sa.
Sannan wani dake dauke da alamun cutar ya shigo Najeriya daga kasashen dake kusa da India.
“ Mun dauki jinin su domin gwajin cutar sannan zuwa anjima za a samu sakamakon gwajin.
Ya yi kira ga mutane musamman baki dake shigowa kasa kuma suna dauke da wasu alamun cutar da su gaggauta kiran wadannan lanbobin domin samun kulan da ya kamata 08000CORONA , 08028971864, 080 35387653, da 0805975886.
Idan ba a manta ba ma’aikatar jihar Legas ta sanar cewa wata ‘yar Najeriya ta kamu da cutar coronavirus.
Matar ta dawo Najeriya daga kasar Britaniya inda bayan ta killace kanta ta je asibiti aka gano tana dauke da cutar.
A yanzu dai mutane uku ne ke dauke da cutar a Najeriya sai dai daya daga cikin su gwaji ya nuna cewa baya dauke da wannan cuta.
Discussion about this post