Gwamnatin jihar Katsina ta ce akwai yiwuwar wani dan asalin jihar ya kamu da cutar coronavirusa. Wanda ake zargin ya kamu ya dawo daga kasar Malaysia ne kuma alamu sun nuna yana dauke da cutar.
Babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Kabir Mustapha ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba.
Ya ce mutumin ya shigo Najeriya daga kasar Malaysia dauke da alamun cutar a jikinsa.
Mustapha yace an killace shi a gida sannan ma’aikatan kiwon lafiya sun dauki jinin sa domin yi masa gwajin cutar.
Ya ce da zaran an samu tabbacin ya kamu da cutar za a fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da shi.
Ya kuma yi kira ga mutane musamman mazauna Dutsen Ma da su tsaftace kan su da muhalli tare da rage shiga taron mutane domin guje wa kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa mutane 8 sun kamu da coronavirus a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa mafi yawan wadannan mutane na da tarihin tafiya zuwa kasashen UK da Amurka.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.
Cutar da ta samo asali a kasar Chana a watan Disemba 2019 ya kama mutane 80,849 sannan da dama sun mutu a kasar.
Coronavirus ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya inda mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.
A yanzu dai kasashen Italiya da Masar a Najiyar Afrika na cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya.