Bayan tabbatar da kamuwar wasu manyan kasar nan biyu, wato Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, akwai bukatar a yi wa gwamnonin Najeriya, ministoci da kuma hamshakin attajiri, Aliko Dangote gwajin Coronavirus.
Abba Kyari ya kamu da cutar bayan ya dawo daga Jamus, shi kuma Bala ya kamu ne bayan ya dawo daga Jamus, haka kuma dan Atiku da yake Asibiti a Gwagwalada.
Shi Bala idan dai daga Jamus ya dauko cutar, to mai yiwuwa ne ya goga wa manyan jami’an Gidauniyar Dangote wannan cuta kenan.
To, kafin Bala ya gana da jami’an Gidauniyar Dangote a ranar Larabar da tawuce a Lagos, sai da ya gaisa da dan Atiku Abukar a filin jirgi, kamar yadda ya bayyana da kan sa a shafin sa na twitter.
Washegari ranar Alhamis kuma Bala ya halarci taron Majalisar Zartaswa ta Kasa, wadda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya shugabanci taron.
Wurin wannan taro kuwa akwai dukkan gwamnonin kasar nan, har ma da Gwamnan Babban Bankin Najieriya, Godwin Emiefile.
Kuma akwai Babban Daraktan Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Okauru, wanda tuni shi da matar sa da iyalan sa duk suka killace kan su, saboda ya halarci taron.
Okauru ya ce dukkan ma’aikatan hedikwatar ofishin gwamnonin Najeriya sun killace kan su, saboda sun halarci taron gwamnonin.
Zuwan Gwamna Bala Jamus
Akalla gwamnoni biyu da suka je Jamus tare da Bala da Abba Kyari, duk sun killace kan su, kuma sun nemi a yi musu gwajin Coronavirus.
Gwamnonin kuwa su ne Godwin Obaseki na Edo da kuma Kayode Fayemi na Jihar Ekiti. Dukkan su sun yi wannan sanarwa a safiyar Laraba.
“Na yi gwajin Coronavirus, bayan gano cewa wasu da muka yi wannan tafiya tare da su, har su biyu sun kamu. Ni dai garau na ke, ba na jin komai a jiki na. Amma na yi gwajin ne, kuma ina jiran sakamako domin na fita daga kangin zargi ko shakku.” Inji Fayemi.
Ministan Gona da Dangote na bukatar gwaji
Ranar Juma’ar da ta gabata, Bala ya gana da Ministan Gona, Sabo Nanono bayan ya gaisa da dan Atiku Abubakar .
Abba Kyari da Dangote
Abba Kyari ya gana da manyan jami’an Kamfanin Siemens, wadanda ake kokarin ganin sun zo sun fara aikin gina cibiyar hasken lantarki a Mambilla, jihar Filato.
A wannan ganawar har da Minsitan Makamashi, Saleh Mamman.
Maimakon Abba Kyari ya killace kan sa da ya dawo Najeriya, sai ya rika gudanar da hidimomin sa ya na ganawa da jama’a daban-daban.
Kyari ya halarci daurin auren dan Sufeto Janar na ‘Yan sanda, da aka yi a kano, ranar 14 Ga Maris.
A wurin wannan taron, Abba Kyari ya gana da Gwamna Umar Ganduje na Kano, Aliko Dangote da kuma Bala Mohammed.
Kwana biyu bayan wannan taron daurin aure da aka yi a Kano, Abba Kyari ya halarci taro a Fadar Shugaban Kasa, kuma har ma ya dauki hoto tare da Shugaba Buhari, kamar yadda ya saba.
An kuma tabbatar da cewa Kyari ya gana da Shugaban Jam’iyyar APC, Adam Oshiomhole da Fadar Shugaban Kasa.
Sannan kuma Kyari ya jagoranci tawagar Fadar Shugaban Kasa, ciki har da Garba Shehu da Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, inda suka je yi wa Gwamna Yahaya Bello ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar sa, Hauwa’u Ozoho.
Zargin Sakaci
‘Yan Najeriya da daman na ci gaba da nuna rashin jin dadin yadda Abba Kyari ya yi ganganci da sakacin barin wannan cutar ta yadu a cikin manyan mahukuntan Najeriya, har a cikin Fadar Shugaban Kasa.
Ana ci gaba da nuna rashin jin dadin yadda ya ki killace kan sa tun bayan dawowar su daga Jamus.
Discussion about this post