CORONAVIRUS: Abba Kyari ya kamu, za a yi wa Kingibe, da wasu jiga-jigan gwamnati gwaji

0

A ranar Talata ne aka ruwaito cewa shima shugaban ma’aikatan fadan shugaban Kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus.

Jaridar Thisday ta wallafa wannan labari sannan wani majiya Mai karfi daga fadar Shugaban kasa da ya nemi a boye sunan sa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa duk da Kyari ya kamu da cutar yana nan cikin koshin lafiya.

” Kwarai da gaske Kyari ya kamu da cutar coronavirus, amma Yana gida cikin koshin lafiya.

Hukumar NCDC ta sanar cewa an samu Karin mutum daya da ya kamu da cutar a Abuja, sannan wasu shida a Legas. A takaice dai mutane 40 ne aka tabbatar sun kamu a Najeriya.

Baya ga Abba Kyari da aka tabbatar ya kamu da wasu da aka dibi jinin su za a yi gwaji, akwai yiwuwar, shima hamshakin attajiri, Aliko Dangote, da Gwamnan Katsina Aminu Masari, duk za a gwada jinin su.

Shima sakataren gwamnati Tarayya da wasu makarraban ofishin sa duk za a yi musu gwajin cutar.

Yadda Kyari ya kamu da Coronavirus

Akwai yiwuwar cewa Abba Kyari ya kamu da cutar ne bayan ziyartar kasar Jamus da yayi ranar 7 ga watan Maris.

Abba Kyari ya ziyarci kasar Jamus tare da ministan Makamashi, ranar 7 ga watan Maris. Sannan suka dawo ranar 14 ga wata. Bayan dawowa daga Jamus sai ya halarci taron bukin babban dan sufeto janar din yan sanda, sannan kuma ya halarci ta’aziyyan mahaifiyar Gwamnan jihar Kogi.

A tawagarsa a kwai ministan makamashi, Saleh Mamman sun dawo kasa Najeriya ranar 14 ga watan Maris.

Tun bayan dawowar sa daga Jamus, Kyari ya halarci taron ta’aziyyan rasuwar mahaifiyar gwamnan Kogi, Yahaya Bello, tare da Garba Shehu, kakakin fadar gwamnati, Sufeto Janar din ‘yan Sanda, Mohammed Adamu da Dangote.

Share.

game da Author