Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanar cewa an samu karin mutane biyar da suka kamu da cutar a Najeriya.
NCDC ta ce biyu na jihar Legas, daya jihar Ribas, biyu a Abuja.
Hukumar ta ce mutane uku sun shigo da cutar daga kasashen waje ne biyu kuma sun kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da wadanda suka kamu.
A yanzu dai mutanen dake dauke da cutar sun kai 51, biyu sun warke sannan daya ya mutu a kasar nan.
Akalla jihohi bakwai ne aka samu tabbacin yaduwar cutar coronavirus a kasar nan.
Coronavirus ta bayyana a kasar nan bayan wani dan kasar Italiya dake dauke da cutar ya shigo Najeriya.
Tun daga wannan lokaci cutar ta fara yaduwa a kasan.
Bisa ga sanarwar hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) mutane 51 ne ke dauke da cutar, biyu sun warke sannan daya ya mutu a kasar nan.
Matakai 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.
Discussion about this post