Cire Sarkin Kano: Zai Yiwu Kuna Kin Abu Amma Alkhairi Ne A Gare Ku, Ko Kuna Son Sa Amma Sharri Ne A Gare Ku, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.

Allah Ta’ala yace:

“An wajabta yaki a kan ku alhali kuna kin sa, zai yiwu kuna kin wani abu amma alkhairi ne a wurin ku. Kuma zai yiwu kuna son wani abu amma sharri ne a gare ku, Allah shine masani, ku baku san komai ba.” [Suratul Bakarah, 216]

A cikin wannan aya, Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bayar da labari, yadda ya umurci bayin sa da suyi yaki, suyi jihadi na gaskiya, ba irin ta’addancin ‘yan Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci ba. Allah ya umurce su da suyi wannan yaki domin kare addini da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a bayan kasa, amma sai mutane suka yi baya, suka nuna cewa basu son yin yaki. Shine sai Allah ya saukar da wannan ayar alkur’ani, yana nuna masu cewa yin jihadin nan shine mafi alkhairi a gare su. Kuma ya nuna masu cewa tana iya yiwuwa mutum ya zamanto yana kin wani abu amma alkhairi ne a gare shi, ko kuma yana son wani abu alhali sharri ne a gare shi. Sai Allah ya nuna cewa a bar masa komai, domin shine yasan komai, mu mutane babu abunda muka sani.

Dalilin da yasa na kawo wannan aya shine, saboda in jawo hankalin al’ummah danagane da abun da ya faru a Masarautar Kano yau, na cire Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi. Mutane kowa yana ta fadar albarkacin bakin sa, tsakanin masoya da makiya. Lallai masoyan Sarki sun shiga damuwa, makiya kuma, musamman mutanen gwamna Ganduje suna ta murna da jin dadi. Amma duk ko ma dai me mutum zai yi, ya sani cewa mu Musulmi ne, kuma mun yi imani da kaddara, mai kyau ko marar kyawo. Domin imanin Musulmi ba zai taba cika ba har sai yayi imani da kaddara mai dadi da marar dadi. Kuma ma’anar imani da kaddara shine, Musulmi ya yarda cewa Allah shine wanda ya tsara dukkanin abun da yake gudana a cikin duniyar nan, kuma ko menene shi. Allah yana sane da abun da zai faru, a yaushe ne zai faru, sannan ta yaya zai faru, da kuma akan wa zai faru. Babu abun da zai faru ba da izinin Allah ko sanin shi ba, mai kyau ne ko marar kyau.

Duk yadda muke son Sarki Sanusi, duk irin kaunar da muke yi masa, wallahi nayi imani da cewa, Allah yafi mu son sa, kuma yafi mu sanin sa, kuma yafi mu sanin me ya dace da shi, kuma shi kadai yasan irin tanadin da yayi masa. Dukkanin mu muna so ya kasance akan wannan gadon sarautar amma Allah da ya halicce shi yana ganin watakila ba alkhairi ba ce a gare shi, shi yasa ya kaddara wannan abun da ya faru, domin yayi masa mafi alkhairin canji da sakamakon da yafi sarautar.

Kuma alhamdulillahi, Sanusi yayi Sarki, yayi shekaru shida akan gadon mulki, kuma har abada ba’a isa a goge sunan sa a jerin tarihin Sarakunan masarautar Kano ba. Idan ana lissafin Sarkunan Kano dole asa da shi. Kuma kamar yadda muka sani, akwai mutane da yawa da suka mutu da burin yin wannan sarauta, amma Allah bai kaddara sun hau ba. Sannan yanzu haka, da yawa daga cikin wadanda aka kulla makarkashiyar cire shi da su, suna son hawa wannan gadon sarautar, amma su sun san da cewa ba za su taba hawan ta ba, haka za su mutu da bakin cikin su. Sannan wallahi na san akwai wadanda za su hau nan gaba, amma su kan su sun san ba zasu taba yin daraja da mutunci irin na Sarki Sanusi ba!

Sannan muna godiya ga Allah, mun ga karshen sarautar Sarki Sanusi a yanzu, sannan bamu san abun da Allah zai yi ba anan gaba. Shi ta shi tayi kyau, amma su ‘yan siyasar da suka yi wannan danyen aiki, da ‘ya ‘yan sarautar da suka goya masu baya aka yi wannan aika-aika, ina rokon Allah ya bamu nisan kwana, ya bamu rai da lafiya, za mu ga nasu karshen da ikon Allah. Ba dai duniya bace? Haba wa, Allah dai ya bamu rai da lafiya, amin. Mutum yayi mai kyau a wannan duniyar yaya ya kare da ita, bare yace shi mugunta da sharri zai shuka a rayuwar sa. Haba ai mu tun da Allah ya bamu Alkur’ani to ya gama muna komai. Labarin komai yana cikin sa, labarin ko wane irin shege da shegiya akwai a cikin sa. Allah ya bamu labarin shedanun masu mulki irin su fir’auna, da masu dukiya irin su karuna, kuma ya bamu labarin karshen su da yadda suka kare.

Kuma shi Sarki Sanusi, wallahi tun da Allah yayi masa sutura, mu sani, cire masa ita bala’i ne ga mai yunkurin yin hakan. Kuma bamu sani ba, watakila wani shiri ne Allah yake son yayi akan sa, shi yasa ya kaddara faruwar hakan.

Da ikon Allah, sai Allah ya bashi wata babbar damar da watakila tafi sarautar. Ya zamanto dukkan wadannan lalatattun makiyan, masu adawa da ci gaba, sai sun dawo daga baya sun fadi a gaban sa, domin neman yayi masu afuwa, kamar yadda ‘yan uwan Annabi Yusuf (AS) suka yi masa daga karshe bayan Allah ya daukaka shi a kan su. Ai ita hassada ga mai rabo taki ce! Kana hassadar mutum shi kuma Allah yana daukaka darajar sa.

Kuma ina kira ga jama’ah da su san cewa, mu dama muna son Mai Martaba Sarki Sanusi ne ba domin mulki ko sarauta ba, a’a, muna son sa ne kawai tsakanin mu da Allah. Don haka wannan abun da suka yi su sani sune a kasa, kuma sune za suyi nadama da dana-sani da ikon Allah. Don haka jama’ah su sani, babu wanda ya isa ya cire son Sarki Sanusi daga cikin zukatan al’ummah. Yanzu ne ma soyayyar za ta karu da ikon Allah.

Allah ya jikan wani mai waka, ya fada cikin wasu baitoci nasa, yake cewa, ‘DA WALAKANCI GARA SHAHADA GA MUSULMI BA ILLA NE BA.’ Lallai wannan haka yake, domin mu wallahi da ace Sarki Sanusi ya tafi gaban wadannan kazaman ‘yan siyasar, masu datti, su walakanta shi, gara su cire shi daga sarautar ya tafi da mutuncin sa yafi. Ana son Musulmi ya zama mai tawadu’u, amma ba’a yarda Musulmi ya wulakanta kan sa ba, har wasu ‘yan daba, ‘yan jagaliya wadanda ba kowan kowa ba su raina shi.

Kuma ina rantsuwa da Allah wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, duk mai hannu a cikin wannan al’amari na cire Sarki Sanusi sai yayi nadama, sai yayi dana-sanin irin gudummawar da ya bayar aka yi wannan. Sannan wallahi, duk mai murna da wannan al’amari, sai murnar sa ta koma bakin ciki da damuwa. Za mu gane irin asarar da aka yiwa Kanawa, da arewa, da Najeriya baki daya. Masu murna su sani, murnar su wallahi sai ta koma ciki.

Sun cire Sarki Sanusi daga sarautar Kano, to su kuwa ku jira, kuga irin tsigewar da Allah zai yi masu!

Sannan ba dai sarautar Kano ba, ga-fili-ga-doki, muna jira muga wanda zai hau ta, kuma ya zamanto ya kai daraja, da mutunci da ilimin Sarki Sanusi. Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau kura.

Sannan wannan badakala ta cire Sarki Sanusi, ta kara fito da dabi’u da halayen mu ‘yan arewa a fili karara, na kwadayin mu, da kin junan mu, da hasadar junan mu, da cin dunduniyar junan mu. Yanzu duniya ta kara fahimtar mu su waye. Kowa yanzu zai kara fahimtar dabi’ar Dan arewa idan ya kai ga mulki, wato baya ganin girma da darajar kowa, baya jin maganar kowa, baya ganin girman manya, baya jin shawarar kowa, kuma kowa baya da mutunci a wurin sa. Da wannan har kullun nike cewa, duk matsalolin da muke fuskanta a arewa, wallahi mu ne da kan mu muka jefa kawunan mu cikin su. Kuma Allah ba zai taba canza muna ba har sai mun canza mugayen halayen mu da munanan dabi’un mu!

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka a koda yaushe.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi. Kuma ina rokon Allah yasa wannan al’amari ya zamanto mafi alkhairi ga Sarki Sanusi, ya musanya masa da mafi alkhairin sa, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author