China ta bai wa Najeriya lakanin kula da masu cutar Coronavirus -Ministan Lafiya

0

Duk da dai har yanzu manyana masana a kasashen duniya 20 na can na kokarin binciken gano maganin cutar Coronavirus, Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce China ta bai wa Najeriya lakanin kula da masu cutar, kuma an gwada an samu nasara sosai a kasar.

“China sun fi kowace kasa dandana kudar Coronavirus, kuma sun samu nasarar warkar da masu cutar da dama. Wannan wasu hanyoyi ne kuma mun rarraba su ga cibiyoyin kula na kasar nan.

” Za a kuma jira sakamako daga kasashen da suka dukufa binciken magani. Duk da dai babu magani, amma China ta yi amfani da wadannan hanyoyi, har an warkar da sama da mutum 20,000, sun murmure, kuma an sallame su.

A karshen makon ne kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta buga rahoton cewa, Masana kimiyya sun fantsama kirkirar magunguna 20 a duniya

Hukumar Kula da Lafiya da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta bada sanarwar cewa masana daban-daban na duniya, sun fantsama kirkiro sinadaran magance cutar Conronavirus.

WHO ta ce har ma wasu masu aikin kirkirar magungunan sun kai ga matakan yin gwaje-gwajen gane tabbaci da kuma ingancin kwayoyin maganin.

Da ya ke har yau babu takamaimen maganin cutar, ya zuwa Asabar ta yadu a kasashe har 49, kuma sama da mutum 2,000 ne cutar ta kashe daga Disamba zuwa karshen watan Maris.

Kasashen Denmark, Estonia, Lithuania, Netherlands da Najeriya duk sun bayyana an kamu da cutar daga kasar Italy a cikin kasashen su.

Ita ma Iran kamar yadda jami’in WHO mai suna Ghebreyesus ya bayyana, mutum 92 daga cikin daruruwan da suka kamu, duk daga waje aka shigar musu da ita.

Tun bayan bullar cutar ce Hukumar Lafiya ta Majalisar Dunkin Duniya (WHO) ta hada kai da Chana, su na hakilon nazarin ainihin yadda cutar ke shiga dan Adam, daga inda can ne asalin ta da kuma irin yadda ta ke mamayewar jiki da kuma irin illar da take yi.

Tun bayan barkewar cutar ne WHO ke ta kokarin wayar da kan kasashen da ta bulla da inda ba ta bulla ba, wajen sanar da su hanyoyin bi domin kauce wa wannan cuta da ta zama ruwan-dare cikin watanni uku.

WHO ta ce ta na wannan kokarin ne kafin jiran magungunan da masana suka dukufa binciken samarwa da kirkirowa.

Share.

game da Author