Hukumar SSS ta bayyana cewa umarni daga fadar shugaban kasa ne ya sa suka tsare Okolie ya sayi wani tsohon layin wayar da ‘yar shugaba Buhari ta taba amfani da shi.
Okolie ya maka hukumar SSS da Hanan a kotu yana neman abi masa hakkin sa da aka tauye masa, aka tsare shi har na tsawon makonni 10 ba tare da an kai shi kotu ba a dalilin siyan layin waya da yayi wanda Hanan Buhari ta taba amfani da shi.
Hanan ta bayyana cewa bata umarci jami’an SSS su kama kowa ba game da tsoho layin ta da wani ke amfani da shi.
Shi dai Okolie ya sayi layin wayar sa salin-alin a kamfani, yana cikin harkokin sa sai jami’an SSS suka damke shi wai ay layin da ‘yar Buhari ne ta taba amfani da shi.
Daga nan aka yi awon gaba dashi aka kulle har na tsawon makonni 10 cur.
Bayan ya fito ne ya kai kara kotu, ya na bukatar a biya shi diyyar tsare shi da aka yi har naira miliyan 500,000,000.
A zaman kotu, Lauyan Hanan ya bayyana cewa babu abinda zai ce game da wannan abu da ale tattaunawa a kotu duk da ya halatta.
Wannan bayani da yayi ya fusatar da Alkalin kotun Nnamdi Dimgba, inda ya ce yaya zai ce babu abinda Hanan zata ce game da abinda yake faruwa bayan har da ita aka maka a kotu.
Shi ko lauyan SSS cewa ba samu takardun cikakken bayanin abinda ya faru ba a dalilin ba zai iya cewa komai ba a kai.
Alkalin kotun ya dage shari’ar sai ranar 3 ga watan Maris domin ci gaba da zama.