BUKIN AMVCA: Za a yi wa Ali Nuhu, Ado Gwanja da wasu fitattu gwajin coronavirus

0

Fitaccen jarumin wasan finafinan Hausa, Kannywood Ali Nuhu ya bayyana cewa NCDC ta gayyace shi domin a yi masa gwajin coronavirus a dalilin halartar bukin karrama jarumai da aka yi a birnin Ikko jihar Legas.

Ali Nuhu da wasu abokan aikinsa hudu suka halarci wannan buki, da aka yi ranar 14 ga watan Maris.

Idan ba a manta ba gwamnatin Legas ta yi kira ga duk wadanda suka hakarci wannan buki su killace kansu na kwanaki 14 domin akwai wanda ya kamu da cutar kuma ya halarci bukin an hole da shi dumu-dumu.

Dubban mutane ne suka halarci wannan taron buki.

A hirar da Ali nuhu yayi da BBC HAUSA ranar Talata ya ce jami’an hukumar NCDC sun ziyarce sa kuma sun bukaci ya bi su ofishinsu domin yin gwajin cutar coronavirus.

Bayan shi, jami’an sun je wurin abokan aikin sa da suka halarci bukin da suka hada da Abubakar Maishadda, Ado Gwanja da Hassan Giggs.

Ali Nuhu ya ce za a yi gwajin ranar talata da dare sannan a sanar dasu sakamakon gwajin ranar Laraba.

Akalla mutane 44 ne suka kamu da cuatar a najeriya zuwa yanzu ciki harda gwamnan Bauchi, Bala Mohammed da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Shima mataimakin Shugaban kasa ya killace kansa na kwanaki 14 a dalilin mua’mula da wanda ya ke dauke da cutar.

Share.

game da Author