Buhari ya umarci El-Rufai ya nada Sanusi mukamai a Kaduna – Bashir Ahmad

0

Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadda shine ke taimaka masa kan harkokin sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa Shugaba Buhari ne ya umarci gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya nada Sanusi Mukamai a Kaduna.

” Har yanzu ban ga wani Yana yabawa Shugaba Buhari ba kan ” Tursasa Dan gaban goshin sa da yayi, Nasir El-Rufai ya yi wa Sanusi Mukamai a Kaduna ba.” Inji Bashir.

Bashir ya rubuta wannan sako ne a shafinsa ta tiwita ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya nada tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi Mukaman mataimakin shugaban hukumar KADIPA da kuma shugaban kwamitin gudanarwar jami’an Jihar Kaduna.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ranar Litini bisa abinda gwamnati ta ce wai ya na karya dokar masarauta da jihar baki daya.

Hakan ya sa gwamna Ganduje ya yatsige shi daga sarautar Kano sannan aka Kora shi lardin Nasarawa.

Sai dai kuma Sanusi ya garzaya Kotu domin kalubalantar korar sa da aka yi zuwa garin Loko, jihar Nasarawa.

Haka kuma Shima tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa tabbas Shugaba Buhari ne ya ingiza Ganduje ya tsige sarki Sanusi, abinda bai yi wa fadar shugaban kasa dadi ba nan da nan Kakakin fadar, Garba Shehu ya fito ya karyata wannan zargi.

Shima tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar ya bayyana cewa lallai da Shugaba Buhari ya saka baki a rashin jituwan tsakanin sarki da Gwamna Ganduje da ba haka ba domin rahoton kwamitin sasanta tsakanin sarki da Ganduje ya ba da shawarwarin da da an bi da ba zai Kai ga tsige sarki Sanusi ba.

Share.

game da Author