Sahihan bayanai daga Jihar Yobe sun tabbatar da cewa wasu mahara da ake zaton Boko Haram ne, sun kashe zaratan sojojin Najeriya 50.
Sun yi wannan mummunar barna ce bayan da suka yi wa sojojin kwanton-bauna a kusa da kauyen Goneri, cikin Jihar Yobe a ranar Litinin.
Majiya daga cikin sojoji ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram din sun kashe kusan ilahirin rundunar sojan atilare guda daya sukutum, a wannan hari da suka kai.
Sojojin na kan aikin sintiri na musamman ne kan hanyar su ta dumfarar Alargamo, sai Boko Haram suka tare su a ranar Lahadi.
An yi ta ba-ta-kashi, inda sojojin suka kori Boko Haram. Washegari Litinin kuma suka sake nausawa gaba, da niyyar karaaawa Alargamo. Boko Haram sun yi musu kwanton-bauna inda suka bude musu wuta da manyan bindigogin da ake harba gurneti da su, wato RPGs.
Majiya ta tabbatar cewa cikin sojojin da aka kashe, akwai masu mukamin manjo biyu, Flight Laftanar na Sojan Sama daya.
Sojojin na kan sintirin Operation Tamonuma ne a lokacin da aka bude musu wuta. An kuma lalata motocin da suke ciki.
Har yau dai mahukuntan sojoji ba su yi magana ba. Yayin da kakakin sojojin Najeriya, Sagir Musa bai maidp amsar tambayar da PREMIUM TIMES ta tusa masa sakon kar-ta-kwana ba.
PREMIUM TIMES ta rike da bayanan wadanda aka kashe. Sai dai ba za ta yi karin bayani ba, har sai bayan hukumar tsaro ta sanar da iyalan mamatan tukunna.