BINCIKE: Gwamnan Kebbi Bagudu, Mantu, Ladan ke kan gaba wajen mallakan kadarorin miliyoyin dala a Dubai

0

Shugaban kungiyan gwamnonin jam’iyyar APC, kuma gwamnan jihar Kebbi ya na daga cikin jerin jiga-jigan ‘yan Najeriya da suke da mallaki kadarorin miliyoyin daloli a Dubai.

Gwamnan Kebbi Abubakar Baguda da aka fi sani da dan gaban goshin tsohon shugaban kasa Sani Abacha, ya yayi kaurin suna wajen harakallar kudaden tsohon shugaban kasa Abacha da ake ta bankadowa.

A binciken kwakwaf da (Carnegie Endowment for International Peace, dake da hedikwata a kasar Amurka ta yi tare da hadin guiwar kamfanin Kadarori da gidaje na Dubai, ta gano wasu ‘yan Najeriya da dama da ke da jibga-jibgan kadarorin miliyoyin dala a Dubai.

Rahoton ya bankado wasu gwamnoni masu ci da wadanda suka sauka 20, sanatoci masu ci da wadanda suka sauka 7 shugabannin ma’aikatun gwamnati, har da kwamishinonin wasu jihohi da ke da mallakin ire-iren wadannan Kadarori a Dubai.

Wasu daga cikin wadannan jiga-jigan sun hada da, Tafa Balogun, Bala Mshelia, Marigayi Ladan Shehu, Samuel Okeke da sauran su.

Bagudu: Rahoton ya nuna cewa Bagudu ya ana da mallakin gidaje har 8 da kudin su ya kai dala miliya 4.8 a Dubai

Marigayi Mohammed Lawal: Tsohon Gwamnan jihar Kwara, ya nada mallakin gidaje 8 da kudin su ya kai dala miliya 2.

Sanata Ike Ekweremadu: Sanata Ekweremadu na da mallakin gidaje har 8 a unguwannin hamshakan kasar da suka kai dala miliyan 7.

Sanata Ibrahim Mantu: Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Nasir Mantu, ya fi shahara cikin wadanda aka gano suna da mallakin kadarorin. Yana da gidaje 12 da suka kai akalla dala miliyan 10.

Ahmadu Ali: Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmadu Ali da matarsa Marian da dansa, Mamman Ali duk suna da mallakin kadarori a kasar. Yana da kadarori 11 da aka yi musu kudi akan dala miliyan 6. Bayannan yana da gida a Landan da kudinsa ya kai dala miliyan 10.

Cecelia Ibru: Tsohuwar shugaban bankin Oceanic, ita ama tana da mallakin kadadrori a Dubai da ya kai dala miliyan 4.3 banda wasu kadarori dabam.

Share.

game da Author