Wani mutum da ba a san ko waye ba ya afka wa shugaban Muhammadu Buhari a garin Kebbi.
Wannan mutum ya afkwa wa shugaba Buhari ne a daidai sun natsu za su dauki hoto a gaban tarin buhunan shinkafa a Kebbi tare da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu da gwamnan jihar Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru.
Ba a san ko menene manufan wannan mutum ba amma kafin ya kai ga damke shugaba Buhari jami’an tsaro su far masa sun kanannande sa sun yi awon gaba da shi.
Buhari dai ya ziyarci jihar Kebbi ne domin halartar bude bukin kamun kifi na Argungu.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=Cr00uSVYVQQ&w=560&h=315]
Discussion about this post