BAYYANAN CORONAVIRUS A ABUJA: Gwamnati ta saka dokar hana tarukan da ya wuce mutane 50

0

Mahukuntan Babban Birnin Tarayya Abuja sun sanar da hana manyan tarukka da ya wuce na mutane 50 a fadin garin.

Hakan ya biyo bayan sanar da bayyanan cutar coronavirus a Abuja da gwamnati ta yi ranar Asabar.

Gwamnati ta ce dole a rage yawan muamula da juna sannan a maida hankali wajen tsaftace muhalli, da jiki.

Haka kuma Suma wuraren bauta wato masallatai da Coci-coci an umarce su day su rage yawan tara jama’a domin dakile yaduwar cutar a kasa baki daya.

Ma’aikatar yin bincike kan cututtuka ta sanar cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

Ma’aikatar ta ce mutum uku daga cikin suna Abuja sannan 7 a jihar Legas. Ma’aikatar ta ce dukan su sun shigo da cutar daga kasashen waje ne a ‘yan kwanakinnan banda guda daya da ya kamu ta hanyar mu’amula da mutane ne.

Yanzu an samu karin yawan wadanda suka kamu a Najeriya zuwa mutane 22 kenan.

Dukkan su na killace a na duba su.

Akalla mutane 12 ne suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya in da wasu 1300, suna killace ana yi musu gwaji. A jihar Katsina ma ana yin gwajin jini wani da ya dawo daga kasar Malaysia da ake zaton yana dauke da cutar.

A dalilin Haka muka kawo muku hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS

1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.

2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.

3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.

4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.

5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.

6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa

7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.

8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.

9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.

10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.

Share.

game da Author