Babban Basaraken Kabilar Yarabawa, Ooni na Ife, ya yi ikirarin yin ‘gwajin’ dandanon maganin Coronavirus.
Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, ya yi wannan ikirarun ne a shafin sa ba Instagram ranar Litinin, kwana daya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya jawabin daukar matakan hana walwala a Lagos, Abuja da Bihar Ogun, domin a shawo kan cutar Coronavirus da ke neman barkewa a Najeriya.
Coronavirus wadda ta kashe sama da mutane 35, 000 a duniya, har yau ba a samo maganin ta ba, amma dai mashahuran masana kimiyya na can na ta kokarin gano maganin cutar, wadda ta fara kunno kai a birnin Wuhan da ke gundumar Hubei na kasar Sin.
An gwada maganin Chloroquine da Hydroxechroquine a bisa tunanin ko za su yi aiki, amma tuni manyan likitoci da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka yi kakkausan gargadin cewa a guji amfani da su, domin ba maganin cutar su ke yi ba.
Ooni wanda ke da masarauta a Ile Ife, garin da aka hakkake cewa shi ne asalin kabilar Yarabawa baki daya na duniya, ya ce ya samu ilhamar yin amfani da wasu hade-haden magunguna da suka warkar da Coronavirus.
Adeyemi ya ce tun a ranar 6 Ga Yuni, 2019 ya samu ‘wahayin’ sanarwar zuwan cutar Coronavirus, lokacin da ake Bukin Al’adun Ifa na Duniya, da aka fi Sani da Orura Meji.”
“Dama tun a lokacin bukin mun fada cewa wata cutar da ba san ta ba A ta barke, amma da yawan mutane ba su dauki gargadin mu da muhimmanci ba. To ku sani dai Edo’s/Urium da Thurim suk akwai au a cikin littattafan addinin da aka saukar.
“Ni a kan wannan gadon sarauta, ina da alaka da kusanci da kasashen duniya, musamman kasar Cuba, Shekaru daruruwa baya, Cuba ta yi riko sosai da tasirin tushen al’adarmu. Dalili kenan suka yi wa sauran kasashe rata da yawa a fannin binciken magunguna.
“Shi ya sa a yanzu da duniya ke cikin wani mawuyacin haki, Cuba ce kadai ta na taimaka wa wasu kasashe.”
Basarakwen wanda a baya ya sha furta kalamai da ke da nasaba da kasassaba, izgilanci ko sabo, ya ce maganin na sa garanti ne, sahihi kuma ingantacce, domin har gwada shi aka yi. Kuma an ga aikin sa.
“Ni da kai na na gwada naganin kuma na gwada shi a jikin wasu masu fama da cutar Coronavirus din. Mun gamsu da aiki da ingancin maganin.” Cewar sa.
Daga nan sai ya kalubalanci masana magunguna na Najeriya da duniya baki su hada kai da shi, su gwada maganin, wanda hadin gargajiya na ganyaye itatuwa ne, domin a samu maganin cutar Coronavirus.
“Na tara tulin maganin domin amfanin al’umma kuma a yanzu haka ina kuma aiki kafada-da-kafada da Yem Kem, domin sayar da maganin a fadin duniya.
Hade-haden Itatuwa Maganin Coronavirus’ -Ooni na Ife
Itacen akoko
Ganyen darbejiya
Albasa
Gamshe/Gazama
Adiran
Barkono
Bita-lif
Sinadarin sulfur
Sai dai basaraken bai kayyade sai nawa za a sha da safe, da rana ko da dare ba.
Kuma bai kayyade shin cikin cokali ko cikin kofi za a rika kwankwada ba.
A Najeriya dai NAFDAC ta bai shawarci oamfanin hada magunguna na May & Baker su samar da Chroloquine mai yawa, a jaraba ko za ta iya magance Coronavirus.
Shugabar NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta ce Chroloquine maganin zazzabin malariya ne, kuma alamomin ciwon Coronavirus ya yi kama da alamomin kamuwa da ciwon zazzabi.
Haka shi ma Shugaban Amurka Donald Trump ya kawo shawarar a yi amfani da Chloroquine, amma tuni manyan likitocin kasar suka gwasale shi.
Discussion about this post