Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya bayyana cewa bashi da burin yin takarar shugaban kasa a 2023 bayan shugaba Buhari ya kammala wa’adin sa.
Ana ta rade-radin cewa Fayemi na shirin fitowa takarar shugaban kasa a 2023 a kafafen sada zumunta na yanar bgizo.
Wasu har ma suna fadin wai gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ne zai fito yayi masa mataimaki a lokacin.
Sai dai kuma a safiyar Juma’a kakakin gwamna Fayemi Segun Dipe a wata takarda da ya fitar ya bayyana cewa babu wannan magana kwata-kwata a gaban su.
” Fayemi na mulkin jihar Ekiti, kuma shine a gaban sa yanzu, babu wani abu da ya sa a gaba fiye da haka. Amma kuma maganar wai zai yi takarar shugaban kasa a APC a 2023, ba gaskiya bane.
” Lallai babu wannan batu, kuma duk inda aka ji shi ba gaskiya bane.
Idan ba a manta ba Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa duk da jam’iyyar bata ce ga yankin da za ta yi shugabancin Najeriya bayan Buhari ba, a na shi ra’ayin ya fi dacewa a ce dan kudu ne ya dare kujerar shugabancin Najeriya bayan Buhari.
Ya ce haka zai sa a samu hadin kai a kasa da kuma wanzuwar dimokradiyya. El-Rufai ya ce ko shi ma zai mara wa wannan zabi idan lokaci yayi.