Bamu cikin tashin hankalin coronavirus – Ali Nuhu

0

Jarumin Kannywood Ali Nuhu ya bayyana wa BBC HAUSA cewa jami’an hukumar NCDC da suka bukaci su yi gwajin jinin sa da na abokan aikin sa sun ce su ci gaba da hidimomin su kawai. Sunce masu sai dai idan sun ji wani abu a jikin su na rashin lafiya sai su gaggauta kawo kansu.

“Sun ce mu kebe kanmu za su zo su dauki samfurinmu kuma har yanzu da na yi maka magana basu zo sun dauki samfurin namu ba… su kansu sun gane cewa wannan maganar karya ce,”

” Jami’an hukumar NCDC sun shaida mana cewa mu ci gaba da harkokinmu ba tare da wata fargaba ba. Sun gaya mana idan mun ji wani abu da yake damunmu mu sanar da su.” inji Ali Nuhu.

Idan ba a manta ba, Ali Nuhu da abokan aikin sa su hudu sun shiga cikin rudani bayan jami’an hukumar NCDC sun bukaci su mika kan su a gwada su ko sun kamu da coronavirus.

Hakan ko ya biyo bayan, halartarbukin karrama jarumar fina-finai da aka yi ne a jihar Legas ranar 14 ga watan Maris.

Bayan wannan taro an gano wani da ya halarci taron da ke dauke da cutar coronavirus.

Hakan ya sa gwamnati jihar Legas yin kira ga duk wadanda suka halarta da su gaggauta garzayo wa a yi musu gwajin cutar.

Ado Gwanja, Hassan Giggs, da Abubakar Maishadda ne suka halarci bukin.

Share.

game da Author