Ba mu da bayanan yadda aka kashe dala bilyan 5 din kudaden Abacha da aka karbo – Malami

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana wa kungiyar SERAP cewa ba ta san yadda aka kashe makudan kudaden daga aka karbo har dala bilyan 5, daga kudaden da Abacha ya kimshe kasashen waje ba.

Gwamnati na magana ne a kan kudaden da aka karbo a tsakanin shekarun 1999 har zuwa 2015.

Haka nan kuma ta ce ba ta san takamaimen adadin kudaden da Abacha din ya kwasa ya boye a asusun bankuna daban-daban a kasashen waje din ba.

Wannan bayani dai ya na kunshe ne a cikin amsar da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya aika wa Kungiyar Rajin Sa-ido Da Bin Diggigin Yadda Gwamnatin Ke Kashe Kudaden Jama’a Bisa Ka’ida (SERAP).

Idan za a tuna, SERAP ta aika wa Ministan Shari’a Malami wasika, shi da Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, inda ta nemi a ba ta cikakken bayanin adadin kudaden da Abacha ya kimshe kasashen waje, da kuma yadda aka kashe sama da dala bilyan 5 na kudaden Abacha da aka maido a Najeriya tun daga 1999.

Ba Mu San Yadda Aka Kashe Na Gwamnatocin Baya Ba – Malami

SERAP ta ce har yau Malami ne kadai ya maida wa kungiyar amsa, mai dauke da bayanin cewa: “Mun bincika ko’ina a wannan ma’aukata, amma ba mu gano takamaimen adadin kudaden da Abacha ya sace ba. Kuma ba mu gano wani rekod na yadda aka kashe dala bilyan 5 da aka dawo wa Najeriya da su, tsakanin 1999 zuwa 2015 ba.”

SERAP dai ta ce tun a ranar 26 Ga Fabrairu Malami ya maida mata amsar wadannan bayanai, amma kuma sai a ranar 9 Ga Maris sannan wasikar ta isa ga kungiyar.

Ga Yadda Muka Kashe Kudaden Abacha Da Wannan Gwamnatin Ta Karbo -Malami

“To amma ina mai sanar da SERAP cewa wannan gwamnati ta karbo dala milyan 322 daga gwamnatin Switzerland a cikin 2018. Kuma an kashe kudaden wajen gudanar da Ayyukan Inganta Rayuwar Marasa Galihu, wato Social Intervention Programme (SIP).

“Sannan kuma akwai wasu dala milyan 308 da ake kan hanyar maido wa Najeriya daga Tsibirin Jersey da taimakon kasar Amurka. Su kuma wadannan kudaden, tuni har gwamnati ta tsara cewa za a kashe su ne wajen gudanar da ayyukan raya kasa da suka hada da: Karasa babban titin Lagos zuwa Ibadan, karasa titin Abuja har zuwa Kano da kuma karasa ginin Gadar Kogin Neja.”

SERAP Ba Ta Gamsu Da Bayanan Malami Ba

Kungiyar SERAP ta bakin Mataimakin Darakta, Kolawole Oluwadare, ta nuna rashin gamsuwar ta da bayanan Minista Malami, tare da cewa da gangan aka ki fito da bayanan adadin kudaden da Abacha din ya sata. Sannan kuma ta ce akwai dungu a bayanan dala milyan 630 da wannan gwamnatin ta ce ta karbo din tun daga watan Janairu, 2018.

Za Mu Maka Gwamnatin Buhari Kotu -SERAP

A ranar Lahadi, 15 Ga Maris, SERAP ta maida amsar cewa, “ganin yadda Ministar Harkokin Kudade ta yi kememe ta ki maido mata da masa kiri-kiri, na bayanan yawan kudaden da yadda aka kashe su, to mataki na gaba da kungiyar za ta dauka shi ne maka gwamnatin Buhari kotu, domin a tilasta mata bayyana wa al’ummar Najeriya adadin kudaden da kuma yadda aka kashe su.”

Amsar da Minista Malami ya bai wa SERAP mai lamba MJ/FOI/REQ/035/11/34 dai na dauke ne da sa hannun Hamza Omolara, Babban Mashawarcin Ma’aikatar Shari’a a Al’amurran Shari’a.

Idan an tuna SERAP ta rabuta wa ma’aukatun biyu wasukun sanin bayanan:

Yadda aka kashe kudaden da aka amso na wadanda Abacha ya sace ya kimshe kasashen waje.

Neman sanin adadin da kowace gwamnati ta karbo daga kudaden Abacha daga 1999 zuwa 2020.

Neman sanin takamaimen ayyukan da aka yi da kudaden dalla-dalla.

Neman sanin wararen da aka yi ayyukan da aka ce an yi din a dukkan inda aka ce an yi aikin.

Neman sanin sunayen kamfanonin da aka bai wa kowace kwangilar gudanar da ayyukan.

Da kuma neman sanin adadin kudin da aka yi kowace kwangilar daki-daki tare da gamsassun takardun bayanan yadda aka aiwatar da komai dalla-dalla.

Share.

game da Author