Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa akwai yara sama da miliyan uku da ba su yi allurar rigakafi ba a kasar nan.
Ehanire ya fadi haka ne a taron kaddamar da shirin inganta yi wa yara allurar rigakafi da aka yi a Abuja.
Taken wannan shiri shine ‘Integrated Medical Outreach Programme (I-MOP)’ sannan hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na kasa (NPHCDA) ta kirkiro shirin.
NPHCDA ta kirkiro wannan shiri ne domin inganta yiwa yara allurar rigakafi da inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko musamman a yankunan karkara.
Shirin zai yi aiki a kananan hukumomi 409 dake fama da matsalolin kiwon lafiya a kasar na.
Za a fara yi wa yara allurar rgakafi daga 3 zuwa 27 ga watan Maris, sannan kuma daga ranar 20 zuwa 24 ga watan Afrilu sai kuma daga ranar 1 zuwa 5 ga watan Yuni.
Ministan kiwon lafiya yace sakamakon bincike ya nuna cewa kashi 33 bisa 100 na yaran dake kasar nan ne kawai aka yi wa allurar rigakafi.
Ya ce domin kawar da irin haka gwamnati ta tsara shirin ‘The National Emergency Coordination Centre (NERIC)’ domin ganin an yi wa duk yara allurar rigakafi a kasar.
Ehanire ya kara da cewa duk da haka an samu ci gaba a kasar domin sakamakon binciken da NDHS ta gabatar ya nuna cewa an ci gaba wajen yi wa yara allurar rigakafi daga kashi 38 a shekarar 2013 zuwa 50.4 a shekaran 2018.
Shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shuaib yace gwamnati na da sauran aiki a gabanta idan har dai tana son samar wa mutane kiwon lafiya na gari a farashi mai sauki.
Ya ce a dalilin haka za a ci gaba da kirkiro shirye –shirye irin haka domin gwamnati ta cimma burin ta.