Wasan tagwayen Manchester da aka doka a ranar Lahadi a kasar ingila ya ba masu kallo mamakin gaske ganin yadda Manchester United ta ladabtar da takwaranta, Manchester City a gida.
Wasan wadda aka buga a gidan Manchester United ya daku matuka.
Tun a farkon zagayen lokaci Manchester ta zura kwallo daya a ragar Manchester City ta hannu mai buga mata gaba, Martial.
Rama wannan kwallo ya gagara wa Manchester City da hatta gogan su dake buga gaba, wato Aguero sai da kociyan su Pep ya canja shi.
A daidai minti 10 a gama wasa sai Manchester City ta saka dan wasan ta mai buga gaba, Ighalo wadda dan Najeriya ne ko zai dinke mata wasan.
Manchester City dai ta yi ta kokarin rama wa wannan kwallo amma inaaa, wankin hula ya kai su dare.
A daidai za a hura usur din tashi, sai United ta jefa kwallo ta biyu ta hannun dan wasanta Dominic a ragar City, kurunkus, aka tashi Wasa.
Wasa ta yi kyau ga magoya bayan Manchester United.