Jam’iyyar APC ta dawo da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa, Sanata Lawali Shuaibu da mataimakin jam’iyyar na yankin Arewa maso Yamma, Inuwa Abdulkadir jam’iyyar.
Shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole ya bayyana haka bayan kammala taron jam’iyyar da aka yi a Abuja ranar Talata.
Oshiomhole ya ce jam’iyyar ta duba laifukan da suka aikata da yayi sanadiyyar aka dakatar da su a wancan lokaci, yanzu jam’iyya ta yafe musu.
Idan ba manta ba an dakatar da Lawali Shua’iabu ne a bisa zargin yayi wa jam’iyyar zagon kasa a lokacin zabe inda yayi wa wata jam’iyya aiki. Shi kuma Inuwa Abdulkadir laifin sa shine dakatar dashi da gundumarsa suka yi a Sokoto wanda haka ya maida shi ba dan jam’iyya ba.
A taron ranar Talata din shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole ya roki gafaran ‘ya’yan jam’iyyar akan laifukan da ake zargin ya aikata.
Idan ba’a manta ba wasu ‘ya’yan jam’iyyar sun maka Oshiomhole a kotu inda suka roki kotu ta dakatar da shi daga ci gaba da shugabancin jam’iyyar.
Bayan hukuncin dakatar da shi da kotu tayi a Abuja. Oshiomhole ya garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci.
Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin Kotun Abuja inda ta ce Oshiomhole ya ci gaba da zama a kujerar shugabancin jam’iyyar APC har sai an kammala shari’a.
A taron jam’iyyar da aka yi a ranar talata, Oshiomhole ya roki ‘ya’yan jam’iyyar da su yi hakuri da shi yanzu ya gano kurakuran sa kuma zai gyara su.
” Yanzu na gane ba ni bane shugaban Jam’iyyar da ya fi kowa iyawa a duniya, kuma ba zan taba zama, Amma kuma babu wanda zai kalubalanci kishin jam’iyya da nake da shi da dagewa wajen ganin jam’iyyar ta yi nasara.
” Na gane cewa yadda na ke rokon jam’iyyar ba yadda wasu ke so bane, wato irin nawa ba irin nasu bane. Saboda haka zan karkato da akala ta suma su karkato na su mu hadu a tsakiya domin a samu jituwa.
Haka Oshiomhole ya fadi da ya ke hira da manema labarai, ranar Talata bayan ganawar ‘ya’yan jam’iyyar.