An yi wa mata miliyan 19.9 kaciya a Najeriya – UNICEF

0

Asusun kula da al’amuran yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta da kafa dokoki da za su taimaka wajen kare budurci da mutuncin mata a kasar.

UNICEF ta yi wannan kira ne a taron tattauna hanyoyin dai-daita jinsin mata da maza a fannonin rayuwa da aka yi a Abuja a makin jiya.

An shirya wannan taro ne domin tunatar da gwamnatocin duniya kan cika alkawarin da suka dauka shekaru 25 da suka gabata a Beijing kan kare budurci da mutuncin mata a duniya.

Taron ya tattauna matsayin wannan alkawari da gwamnatocin duniya suka yi inda ta yanke shawarar cewa dole sai an mike tsaye wajen kare mutuncin mata a duniya.

Wani sakamakon binciken da UNICEF ta gudanar ya nuna cewa ana yi mace daya cikin ‘yan mata 20 masu shekaru 15 zuwa 19 fyade a duniya.

Binciken ya kuma nuna cewa daga cikin wannan kaso kashi biyu ne kawai daga cikinsu ke samun kulan da ya kamata a Najeriya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa an samu raguwan yawan ‘yan mata da basu zuwa makarantan boko da ya kai miliyan 79 a duniya shekaru 20 da suka gabata.

Sai dai hakan bai hana ana yi musu fyade ba, auren wuri ko kuma kaciya da haka ke cutar da rayuwarsu matuka.

UNICEF ta gano cewa a Najeriya an yi wa mata miliyan 19.9 kachiya sannan miliyan 12 sun yi auren wuri.

Illoli shida dake tattare da yi wa mace kaciya.

1. Hana mace jin dadin jima’i.

2. Hana haihuwa.

3. Kamuwa da cututtuka irin na sanyi da yake kama gaban mace.

4. Kawo zuban jini wajen haihuwa wanda ka iya kawo ajalin mace.

5. Kawo laulayin haila

6. kawo doguwar nakudar haihuwa

Share.

game da Author