An rage jaridun da ke dauko rahoto a fadar shugaban kasa daga su 100 zuwa su 13 rak

0

Fadar Shugaban Kasa ta zabtare yawan wakilan kafafen yada labarai masu dauko rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya ce daga wannan rana ba za a sake barin 87 daga cikin su 100 su riga shiga Fadar Shugaban Kasa ba.

Ya ce an yi haka ne domin a takaita yiwuwar kamuwa da cutar Coronavirus, wadda a yanzu haka ta kama Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.

Ya ce ba a yi haka don.hana kafafen yada labarai dauko rahoto ba. A cewar sa, hakan ya yi daidai da ka’idar da Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa ta gindaya a Abuja cewa kada mutane sama da 50 su rika taruwa a wuri daya.

Kafafen yada labaran da aka amince su ci gaba da dauko rahotannin kafin a dakile Coronavirus, sun hada da Gidan Radiyon FRCN, NTA, VON, NAN, wadanda duk na gwamnati ne.

A rukunin wadanda ba na gwamnati ba. an amince da jaridar Sun, Channels TV da kuma TBC.

Sun ta Uzor Kalu ce, wanda ke daure, kuma daga jaridar ce Buhari ya dauki Femi Adesina a matsayin kakakin yada labaran sa.

It’s kuma Talbijin din TVC ta jigon jam’iyyar APC ce, Bola Tinubu.

Shehu ya ce sauran wadanda aka hana shiga, duk za su rika samun labaran abubuwan da suka faru a wurin sauran wadanda aka yarda su rika shiga.

Shi ma Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida masu dauko labarai a Fadar Shugaban Kasa, an amince ya shiga.

Akwai masu dauko hoto daga jaridun Vanguard da Thisday da aka amince su ci gaba.

Share.

game da Author