An nada Shugabannin Zartaswa bayan dakatar da Oshiomhole

0

Tuni dai jam’iyyar APC ta nada sabbin shugabannin zartaswa sa’o’i kadan bayan da kotu ta dakatar da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole, kuma ta hana shi sake shiga harabar Hedikwatar Sakateriyar APC ta Kasa.

Yayin da aka nada Waziri Bulama a matsayin Sakataren Riko na Kasa, amma kuwa Salihu Mustapha ya nuna tankiya da jayayyar nada Bulama, wanda a cewar sa Oshiomhole ne ya bada umarnin nada shi, bayan kotu ta rigaya ta dakatar da shi.

Dalili kenan ya ce duk wani abu da za a aiwatar da sunan Oshiomhole, to haramtacce ne, kuma an karya doka da umarnin kotu.

An nada Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo a matsayin Mataimakin Shugaba Na Kasa Shiyyar Kudu, sai kuma Paul Chukwuma a matsayin Mai Binciken Kudin Jam’iyya na Kasa.

An Shigar Da Karar Kin Yarda Da Shugabancin Ajimobi a Kudu

Ana wata kuma sai ga wata. Wani shugaban jam’iyyar APC na karamar hukuma a jihar Ekiti, mai suna Micheal Akinyele, ya shigar da karar rashin amincewa da nada Ajimobi a matsayin Mataimakin Shugaban APC na Shiyyar Kudu.

Ya zargi Oshiomhole da cewa shi ne ya kakaba sunan Ajimobi, yayin da Akinyele din da Gbenga Aluko su ma sun nemi mukamin, tun bayan da wanda ke rike da mukamin a baya, wato Niyi Adebayo, aka nada shi Ministan Cinikayya, Kasuwanci Da Zuba Jari.

Share.

game da Author