Ranar Alhamis din nan aka yamutsa gashin baki a Zauren Majalisar Dattawa, kafin amince wa Shugaba Muhammadu Buhari ya ciwo bashin dala bilyan 22.
Hakan kuwa ya biyo bayan shawarar da Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Lura Da Basukan Cikin Gida da Waje ya bayar.
Shugaban Kwamitin, Clifford Ordia, dan PDP daga Jihar Edo, ya karanto rahoton kwamitin, inda kuma ya nemi Majalisar Dattawa ta amince a ciwo bashin.
Sai dai kuma bikatar a tattauna batun ba a gaban ‘yan jarida ba, ya haifar da ka-ce-na-ce tsakanin dattawan majalisar da kuma Shugaban Majalisa Ahmad Lawan, har tsawon fiye da minti 30.
Shugaban Masu Rinjaye, Abdullahi Yahaya da Shugaban Marasa Rinjaye, Enyinnaya Abaribe, sun bada shawarar ya fito a yi wa majalisa bayani dalla-dala na komai batun karbo bashin ya kunsa.
Sai dai shi kuma Lawan ya jajirce ya kawo wani kabli-da-ba’adi daban.
An ci gaba da tabka gardama da musayar yawu har dai Lawan ya kara tirjewa ya ce sai dai a yi kamar yadda tun farko ya ce hakan za a yi.
Bayan an dan yi shiru kamar na minti biyar kuma an tuntubi juna, sai Yahaya ya nemi a yi bayanin a asirce, kuma aka amince din.
Tun dai cikin watan Nuwamba, 2019 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisa ta wancan lokacin neman amincewa ya ciwo bashin dala bilyan 22 domin gudanar da ayyukan raya kasa.
Tun tuni ya kamata a ce an yi wasu ayyukan raya kasa tsakanin 2016 zuwa 2018, amma ba a yi ba saboda karancin kudaden shiga.
To wadancan ayyukan da ba a samu sukunin yi ba ne za a yi da wadannan kudade idn an ramto su.
Shugaba Buhari ya aika wa Majalisa a zamanin Bukola Saraki neman amincewa a ciwo bashin na dala bilyan 30 a lokacin, amma aka ki amincewa.
Tsohon sanata Shehu Sani ya bayyana cewa sun ki amincewa da ciwo bashin a wancan lokacin domin hana Najeriya ruftawa cikin ramin matsalar tattalin arzikin da ba ta iya fitowa idan bashi ya cika mata ciki.
A halin da aka ciki dai a yanzu, kudaden da Najeriya ke samu a duk wata masu dimbin yawa na tafiya ne wajen biyan bashin da gwamnatin Buhari ke ta ciwowa babu daga kafa.
Discussion about this post