An gurfanar da saurayin da yayi wa Akuya fyade a kotu

0

Wani matashi mai shekara 22 ya fada hannu ‘Yan sanda bayan zargin fyade da yayi wa wata Akuya a gari Ado-Ekiti.

Dan sandan da ya shigar da karan Olubu Apata, ya bayyana cewa an kama Sunday ya na aikata wannan abu ne a unguwar Basiti dake Ado-Ekiti.

Mai shigar da kara ya ce bayan Sunday yayi wa Akuyar fyade sai ta mutu nan take.

A karshe ya Sunday ya musanta aikata haka sai dai kuma Alkalin kotun ta bada belinshi akan Naira 50,000 sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Maris.

Share.

game da Author