An damke yarinyar da ta luma wa mutumin da ya yi kokarin yi mata fyade wukar fere doya

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Bala Elkana ya bayyana cewa sun damke wata yarinya mai shekaru 16 da aka kama da laifin kashe wani mutum mai suna Babatunde Ishola saboda danneta da ya nemi yi da karfin tsiya.

Elkana ya fadi haka ne ranar Lahadi inda ya kara da cewa wannan abin takaicin ya faru ne ranar Asabar a gidan mamacin dake zama a Ogundele Aboru jihar Legas.

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Babatunde mai shekaru 44 na aikin gadi a makarantar sakandaren da wannan yarinya ke karatu kuma shi abokin mahaifin yarinyar ne.

Dama kuma Babatunde ya dade ba shi da mata, shi kadai yake zama a gidansa.

Ita dai wannan daliba kan garzaya gidan Babatunde ta na taya shi dan aikace-aikace kama share-share ne, wanke-wanke da sauransu da fere doya idan yana jin yunwa.

Wata rana da wannan yarinya ta je gidan sai Babatunde ya rarumeta da karfin tsiya ya na neman ya danneta wato yayi lalata da ita.

Wannan yarinya ta dauki wata sharbebiyar wukar fere doya tako luma masa a ciki, nan take ya yanke jiki ya fadi gawa.

Ita dai wannan yarinya ta aikata haka ne cikin tsoro da rashin sani.

Elkana yace sun kama yarinyar da wukar da ta yi amfani da shi sannan sun kai yarinyar asibiti domin a duba lafiyar ta tukunna.

Sashen dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na rundunar za ta ci gaba da bincike akan wannan lamari kafin ta dauki mataki.

Share.

game da Author