Rundunar ‘yan sandan jihar Barno ta kama sifeto Abubakar Musa da laifin yi wa yara mata kanana biyu fyade a jihar.
Mahaifiyar yaran Hadiza Saidu ta kai kara ofishin ‘yan sanda inda ta bayyana cewa Musa ya yi lalata da yaranta mata kanana da ke da shekaru 10 da 12.
“ Musa kan lallabo ya shigo gidan mu bayan ya tabbatar babu wani babba a gidan sai yayi lalata da daya sannan ya rika cusa yatsun sa a gaba dayan.
Hadiza ta ce yaran nata da kansu ne suka gaya mata abin da wannan dansanda yake yi da su.
“ A lokacin da zan kawo kara ofishin ‘yan sanda abokan aikin Musa sun roke ni kada na kawo kara saboda kada a kore shi daga aiki. Amma kuma dole in kawo karar sa saboda irin munin abinda yayi.
Kakakin rundunar Edet Okon ya tabbatar da aukuwar hakan inda ya musanta rade-radin da wasu ke yi cewa wai jami’an tsaro na kokarin shashantar da maganar.
Okon yace Musa na nan tsare a ofishin su kuma zai ci gaba da zama a tsare har sai an kai shi kotu.
Bayan haka shugaban kungiyar ‘New Nigeria and Youth Empowerment Initiative’ Lucy Yunana ta ce kungiyar za ta bi yi tsayin daka wajen ganin an bi wa wadannan ‘yan mata hakkin su.