ALBASHI: Duk da tashin hankalin coronavirus, likocin Najeriya sun fara yajin aiki

0

Yayin da gwamnatin Najeriya ke kokarin ganin ta hana yaduwar cutar coronavirus a kasar nan kungiyar likitoci (ARD) reshen Abuja sun fara yajin aiki.

Kungiyar ta sanar da fara yajin aikin ne ranar Talata awa daya bayan gwamnatin jihar Legas ta sanar da gano coronavirus a jikin wata mata a jihar.

ARD ta ce sai da ta duba matsalolin rashin biyansu albashi, yadda suke kula da marasa lafiya saboda rashin ingantattun kayan aiki sannan da matsalar da za su iya shiga idan coronavirus ta barke a kasar nan kafin suka fara yajin aikin.

Shugaban kungiyar Roland Aigbovo ya ce sun fara yajin aikin ne saboda rashin biyan su albashin har na tsawon watannin biyu da gwamnati ta ki yi.

Aigbovo ya ce tallauci ta yi wa ma’aikatan su da dama katutu a jika sannan duk da barazanar shiga yajin aikin da suka yi gwamnati ta yi watsi da bukatar su.

Ya ce sauran ma’aikatan asibiti da basu samu albashi ba za su bi sawun su nan da awa 48 idan har dai gwamnati bata yi komai ba.

Aigbovo yace ma’aikatan kiwon lafiya a Abuja sun tsinci kansu a wannan yanayi ne tun da gwamnati ta ta fara amfani da tsarin albashi da IPPIS.

Gwamnati ta shigo da tsarin biyan ma’aikatan gwamnati albashi da tsarin IPPIS domin kama masu cin rashawa ta hanyar karbar kudaden wadanda ba su aiki wato ma’aikatan karya.

Share.

game da Author