Gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum ya jinjina wa wata malamar makarantar firamare dake jihar bisa maida hankali da tayi a wajen aikin ta na malunta.
Wannan malama wacce ‘yar asalin jihar Abia ce ta shekara 31 tana karantarwa a makarantar firamare na Kyarimi da ke Maiduguri.
Ko da gwamna Zulum ya kai ziyarar bazata wannan makaranta da misalin karfe 6:30 na safe, sai ya iske babu kowa a makarantar, babu malami, ko dalibi ko da guda daya ne kuwa.
Amma kuma abin mamaki sai ya iske wata malama ita kadai tilo ta na zaune tana jiran dalibai.
Gwamna Zulum ya tambaye ta ko ‘yar asalin wane jiha ce ita? Sai ta shaida masa cewa ita ‘yar asalin jihar Abia ce amma kuma ta shekara 31 tana karantarwa a jihar Barno.
Daga nan sai gwamna Zulum ya yaba mata sannan yayi mata kyauta kuma yayi mata albishir cewa lallai gwamnati ba za ta manta da ita ba ko bayan ta yi murabus a aiki sannan yayi mata dan ihsanin da ba a rasa ba.
Mutane musamman ‘yan asalin jihar Barno suna yabawa salon mulkin gwamna Zulum a jihar, inda suke cewa lallai tsohon gwamna Kashim Shettima ya yi musu zabin mutum nagari a matsayin gwamnan jihar.
Zulum ya maida hankali matuka wajen inganta jihar da mutanen ta.