Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa an samu karuwan adadin yawan mutanen dake kamuwa da zazzabin lassa da yawan dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar.
Hukumar ta ce daga watan Janairu zuwa Fabrairu mutane 689 ne suka kamu da cutar sannan wasu 118 sun rasu.
An samu wannan yawa ne daga kananan hukumomi 115 dake jihohi 27 a fadin kasar nan.
Har yanzu dai jihohin Edo, Ebonyi da Ondo ne jihohin sa suka fi fama da wannan cuta.
YADDA ZA A KIYAYE DAGA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA
1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.
2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.
3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.
4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
5. Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.
6. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.
7. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.
8. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.
9. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
10. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
11. Kona Daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
12. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.