Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa an samu kari a yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan wadanda suka rasu tun da cutar ta bullo a watan Janairu.
Hukumar ta ce a ranar 16 ga watan Fabrairu adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya karu daga 109 zuwa 115.
Haka kuma ya sa aka samu karin yawan mutanen da suka rasu a sanadiyyar kamuwa da cutar daga 70 zuwa 103.
Hukumar ta bayyana cewa an samu wannan kari ne a dalilin rashin bada rahotannin adadin yawan mutanen da suka rasu da yawan wadanda ke fama da cutar.
Duk da haka hukumar ta ce an samu wannan kari ne daga jihohi 17 a kasar nan da suka hada da jihohin Ondo, Edo, Ebonyi, Kano, Kogi, Kaduna, Taraba, Plateau, Bauchi, Enugu, Abia, Benue, Borno, Gombe, Sokoto, Legas da jihar Katsina.
Rahotan ya kuma nuna cewa wasu ma’aikatan kiwon lafiya biyu sun rasu a sanadiyyar kamuwa da cutar a jihohin Bauchi da Katsina.
Hakan ya kawo jimlar adadin yawan ma’aikatan kiwon lafiya da suka rasu a dalilin kamuwa da cuta zuwa 20.
Hukumar ta kuma ce har yanzu jihohin Edo,Ebonyi da Ondo ne suka fi yawan masu fama da wannan cutar.
Discussion about this post