ZAZZABIN LASSA: Ayyana dokar tabaci akan cutar ne mafita a Najeriya – Kungiyar NARD

0

ZAZZABIN LASSA: Ayyana dokar tabaci akan cutar ne mafita a Najeriya – Kungiyar NARD

Kungiyar likitoci (NARD) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ayyana dokar tabaci akan zazzabin lassa ganin yadda cutar ke ta kara yaduwa a kasar nan.

A makon da ya gabata hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ya nuna cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 285 sannan 41 sun rasa rayuwar su a dalilin kamuwa da wannan cuta a kasar nan.

Shugaban kungiyar Aliyu Sokomba yace a dalilin haka kungiyar ta ga ya dace gwamnati ta ayyana dokar tabaci a kan cutar domin karfafa matakan hana yaduwar cutar.

Sokomba ya kuma yi kira ga gwamnati da ta biya ma’aikatan kiwon lafiya alawus din gamuwa da hadari cewa yin haka zai kara karfafa musu guiwowi wajen gudanar da aiyukkan su.

Sakamakon bayanan hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) sai kara nuna yadda zazzabin lassa ke kara yaduwa a Najeriya tun bayan bullowar cutar a watan Janairun 2020 inda mutane 365 suka kamu sannan 47 cikin su suka rasu daga jihohi 23.

Bisa ga rahotan da hukumar ta gabatar a mako na biyar tun da ta bullo a Najeriya ranar Laraba ya nuna cewa jihohin da akalla mutum daya ya kamu da cutar ya karu daga 19 zuwa 23.

Wadannan jihohi sun hada da Edo, Ondo, Bauchi, Barno, Ebonyi, Nasarawa, Kano, Kogi, Kaduna, Adamawa, Cross rivers, Delta, Osun, Ogun,Abia, Taraba, Filato, Gombe, Enugu, Kebbi da Anambra.

Sannan har yanzu jihojin Ondo, Edo da Ebonyi na cikin jihohin da suka fi fama da cutar.

Sai dai kuma an samu ragowa a yawan mutanen dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar domin a cikin mako na biyar mutum shida ne suka rasu a maimakon 19 da aka samu a makonnin baya da suka gabata.

Karuwa a yawan mutane

Hukumar ta rawaito cewa a cikin mako na biyar adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ya karu daga 95 zuwa 104.

An samu karin mutanen ne daga jihohi 15 da suka hada da Ondo, Edo, Ebonyi, Kano, Kogi, Kaduna, Delta, Taraba, Filato, Bauchi, Gombe, Enugu, Anambra da babban birnin tarayya Abuja.

Ma’aikacin kiwon lafiya a jihar Delta ya kamu da cutar kuma wasu ma’aikatan kiwo lafiyar biyar sun mutu a jihohin Taraba, Barno da Kano.

NCDC ta ce tun da wannan cuta ta bullo a farkon shekarar nan mutane 47 ne suka rasu, kashi 12.9 bisa 100 kenan a kididdige.

A takaice dai a shekarar 2020 hukumar ta samu rahotan akalla mutum daya ya kamu da cutar daga kananan hukumomi 74 dake jihohi 23.

Share.

game da Author