ZARGIN GINA GIDAJE: Malaman Jami’o’i sun maida wa TETFund raddi

0

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASSU), ta maida wa Hukumar Kula da Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFund) kakkausan raddi a kan zargin da ta yi cewa malaman jami’a na kashe kudaden da hukumar ke ba su wajen sayen motoci da gina gidaje.

ASSU ta ce “cin zarafi ne da kokarin tozarta malaman jami’a a yadda TETFund ta yi wa malaman kudin goro, ko kuma jam’un da ke nuni da cewa kowane malami ma halin sa ke nan.

Hukumar Bunkasa Ilmi a Manyan Makarantu, ta bayyana rashin jin dadin yadda malaman jami’o’i da na manyan makarantu da cibiyoyin ilmi ke karkatar da kudaden da ita TETFund din ke ba su domin su yi binciken da zai bunkasa ilmi.

TETFund ta ce ta gano yadda dimbin malamai ke karkatar da kudaden su na sayen motoci da saye ko Gina gidaje da wadannan kudade.

Wannan zargi ya fito ne kwanaki kadan bayan Hukumar ICPC ta bankado yadda wasu cibiyoyin ilmi da na kiwon lafiya suke yin aringizon makudan kudade a cikin kasafin kudaden su.

Mataimakin Daraktan Bincike na TETFund, Salisu Bakari ne ya yi wannan zargi ga malaman jami’a, a taron karin sanin makamar aiki da hukumar ke kan shirya wa wasu malamai na jami’o’in Najeriya, a Dubai.

Ya ce su ma jami’o’in dungurugum ba a bar su baya ba wajen karkatar da kudaden bincike.

“Babbar cin amana ce a ba ka kudade domin ka gudanar binciken da zai inganta harkar ilmi ko wani fanni, amma ka karkatar da kudaden wajen data bushashar biyan bukatar ka.

“Mun yi binciken bin diddigi, sai muka bankado yadda malaman jami’o’i ke kwasar kudaden da TETFund ke ba su domin bincike su na sayen motoci da gina gidaje.

Daga nan sai Bakari ya yi dogon bayanin irin matakan da TETFund za ta dauka a kan wannan lamari.

‘Ba Za Mu Bari a Zubar Mana da Mutunci Ba’- ASUU

A wata tattaunawa da Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i na Kasa, Biodun Ogunyemi ya yi da wakilin mu, ya shaida masa cewa kungiyar su ba za ta bari wani mutum ko wata cibiya ta zubar wa malaman jami’a da mutunci a idon duniya ba.

Ya kalubalanci daraktan TETFund da ya fallasa wadanda ya ke zargin sun kashe kudaden binciken bunkasa ilmi wajen sayen motoci da gina gidaje, domin ASSU ta bada hadin kai wajen tuhumar su.

A karshe ya ce bai ce wai babu gurbatattu a cikin malaman jami’a ba, kamar yadda sauran bangarori ko’ina ba a rasa gurbatattu.

“Amma jam’u da kudin-goron da ya yi mana shi ne abin damuwa, saboda zubar mana da kima ya ke neman yi a duniya.” Inji Shugaban ASSU.

Share.

game da Author