ZARGIN ARINGIZO: ‘Yan Najeriya sun fusata da kudin tikitin jirage a Hukumar Tashoshin Ruwa

0

Wata takardar harkallar aringizon kudaden tikitin jiragen sama ga ma’aikatan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, ta fado hannun PREMIUM TIMES.

Wannan takarda ta nuna yadda mahukuntan NPA yadda ake yin aringizon makudan kudaden sayen tikitin jiragen kasa. Hakan ya yi kamari har dimbin jama’a sun rika yin tir da Allah-wadai a kafafen soshiyal midiya.

Hadiza Bala ce Shugabar Hukumar Lura da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).

Takardar wadda aka rubuta dauke da za hannun Babban Manajan Tsare-tsare, A. A Jato, a ranar 4 Ga Janairu, ta na dauke ne da sabon aringizon kudaden tikitin jirage da za a rika cirewa daga aljihun gwamnati ana biya ma ma’aikata.

Takardar ta sanar cewa “an yi wannan kari ne saboda kamfanonin sufurin jirage sun dan yi karin kudin tikiti.

Harkalla Da Aringizo Kiri-kiri

Za a rika gabzar naira 200,000 a matsayin kudin karamin tikitin jirgi daga Lagos zuwa Abuja.

Za a rika wazgar naira 250,000 a matsayin kudin babban tikitin jirgi da Lagos zuwa Abuja.

Za a zabtari naira 200,000 kudin karamin tikitin jirgi daga Lagos Calabar da kuma Benin.

Za a kafci naira 250,000 kudin babban tikitin jirgi daga Lagos zuwa Calabar da kuma Benin.

Za a rika dumbuzar naira 300,000 kudin babban tikitin jirgi daga Lagos zuwa Maiduguri.

Za a rika kamfatar naira 300,000 babban tikitin jirgi daga Lagos zuwa Fatakwal.

Za a rika lodar naira 320,000 da naira 290 kudin babba da karamin tikitin jirgi daga Lagos zuwa Yola.

Karami da babban tikiti daga Lagos zuwa Sokoto kuwa, NPA za ta rika cizgar naira 260,000 da 240,000 daga aljihun gwamnati.

Sai kuma naira 200,000 da 180,000 kudin babba da karamin tikitin jirgi daga Lagos zuwa Owerri.

Lagos zuwa Ilorin kuwa za a kwashi naira 180,000 da 150,000 kudin babba da karamin tikitin jirgi.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa ana sayar da tikitin jirgi daga naira 21,000, amma an yi kari zuwa naira 25,000. Sai kuma babban tikiti karin ya koma kisan daga naira 45,000 zuwa naira 50,000.

Tsuntsun Da Ya Kira Ruwa

Wannan cuwa-cuwar da a ka fara a NPA ta janyo wa Shugabar NPA, Hadiza Bala da Shugaba Muahammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC caccaka, tsangwama da muzantawa a kafafen sada zumunta na soshiyal midiya, musamman tiwita.

Wani shafin tiwita mai suna @ije12002, cewa ya yi, “Wannan ai rashin kunya da rashin mutunci ne. Shin Hadiza Bala ta rattaba hannun amincewa kuwa. Wannan tsiyar ce fa aka rika hantara da zargin Diezani Alison-Madueke ta rika aikatawa.”

NPA Ta Kare Kanta

An yi kokarin samun kakakin yada labarai na NPA, amma abin bai yiwu ba. Ita Hadiza Bala an kira lambar ta, amma ba ta amsa kiran PREMIUM TIMES ba.

Amma Jato, wanda ya sa hannu a takardar ya shaida wa jaridar THE NATION cewa wadannan kudade ba na sayen tikiti kadai ba ne.

Ya ce a ciki akwai kudin harajin-jiki-magayi, kudaden karakaina zuwa filin jirgi da kudaden lalurori idan ma’aikataci ya sauka inda aka tura shi.

“Kuma kai-tsaye ne za a rika biyan wadannan kudade ga kamfaninin sufurin jiragen, ba wait kowa a hannun sa za a damka masa ba.

“Sannan wannan farashi ba kowane ma’aikacin NPA ne za a yi wa shi ba. Sai Shugabar NPA, mambibin Hukumar Gudanarwa da kuma manyan ma’aikata, wadanda dukkan su na ma kida yaushe suke yawan tafiye-tafiye ba. Gaskiyar maganar kenan.”

Share.

game da Author